Birtaniya na duba yiwuwar amincewa da kasar Falasdinawa - Cameron

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon fairaministan Burtaniya kuma sakataren harkokin wajen kasar na yanzu, David Cameron ya ce Burtaniya na da alhakin tsara yadda kasar Falasdinawa za ta kasance.
Da yake bayani ga 'yan majalisar dokin kasar, Mista Cameron ya ce ya zama dole Falasdinawa su nuna "jajircewa" dangane da warware rikicin ta hanyar samar da kasashe biyu na Faladinawa da Isra'ila.
"Domin faruwar hakan, mu tare da kawayenmu za mu duba batun amincewa da kasar Falasdinawa, har ma a Majalisar Dinkin Duniya," kamar yadda ya shaida wa Majalisar masu tsattsauran ra'ayi ta Yankin Gabas ta Tsakiya.
"Hakan ka iya kasancewa daya daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen cimma tsarin."
Mista Cameron ya kuma bukaci Isra'ila da ta bari a kai kayan agaji zuwa Gaza, inda ya kara da cewa "abin takaici" ne a rinka ajiye agajin da Burtaniya da sauran kasashe suka bayar a kan iyaka.
Sakataren harkokin wajen na Burtaniya ya kuma ce shekaru 30 da suka gabata ba su kasance masu dadi ba ga Isra'ila saboda ta gaza sama wa 'yan kasarta tsaron da suke bukata.
Sai dai ya ce ta hanyar fahimtar kuskuren da Isra'ilar ta yi ne kawai zai samar da zaman lafiya da cigaba.
Burtaniya dai ta dade tana fafutukar samar zaman lafiya ta hanyar samar da kasashe biyu.
Mista Cameron ya kuma nuna cewa Burtaniya ka iya ayyana kasar Falasdinawa a lakocin tattaunawa amma ba wai hanyar karshe ta warware rikicin ba But
A wani mataki na yarjejeniya mai dogon zango, sakataren harkokin wajen na Burtaniya ya ce dole ne Isra'ila ta gamsu da an sakar mata dukkannin mutanenta da aka yi garkuwa da su da kuma samun amincin cewa Hamas ba za ta sake kai mata hari ba sannan kuma a tabbatar shugabancin kungiyar ya bar Gaza.
Ya ce cimma yarjejeniya abu ne "mai wahala" amma ba "wanda ba zai yiwu" ba.











