Halin da jaririyar da ta zama mutum na biliyan ɗaya a Indiya ke ciki

An wallafa

An haifi Aastha Arora da misalin karfe 5:05 na asubahin ranar 11 ga watan Mayun 2000 a asibitin Safdarjung da ke birnin Delhi.

An kuma bayyana ta a matsayin jaririyar da ta sanya yawan al'umar Indiya zuwa biliyan daya.

Mutane da dama ne suka je barkar haihuwarta ciki har da wasu daga cikin ministocin gwamnatin ƙasar waɗanda aka ɗauka hoto a lokacin da suke riƙe da jaririyar lulluɓe cikin wani mayafi mai launin ruwan hoda.

Haihuwar Aastha ta sa ƙasar Indiya kafa sabon tarihi, inda ƙasar ta bi sahun China wadda ita ce ƙasa ɗaya tilo da ke da yawan al'ummar da suka haura biliyan ɗaya.

A wani gagarumin biki da aka gudanar a ƙasar na samun cimma wannan matsayi, wakilin asusun kula da yawan al'umma na Majalisar Dinkin Duniya Micheal Vlassoff ya bayyana Aastha a matsayin yarinya ''mai baiwa ta musamman''

Haka kuma jami'ai sun ce haihuwarta ne ya tayar da ƙasar Indiya tseye, domin lalubo hanyoyin da za ta kula da yawan al'umar da Allah ya huwace mata.

Bikin haihuwarta ya ja hankulan kafofin yada labarai na duniya, kuma kwanaki bayan bikin sunanta 'yan jarida da dama sun ta turuwa zuwa gidansu da ke Najafgarh, wata unguwa ta masu matsakaicin hali da ke da yawan al'umma a kudu maso yammacin birnin Delhi

Nima ina cikin tawagar BBC da ta ziyarci gidansu a lokacin domin ganin jaririyar, tare kuma da yi hira da mahaifiyarta Anjana Arora.

Shekaru sama da 20 bayan faruwar hakan, na sake kai ziyara gidan su wannan yarinya domin ganin halin da a yanzu 'yarinyar ta musamman' ke ciki.

Matashiyar mai shekara 22 ita ta bude min kofa a lokacin da na kai ziyara gidansu ranar Lahadi da safe, ta kuma shaida min cewa tuni ta daina daukar kanta a matsayin wata bil-adama ta musamman.

Saboda a cewarta mafi yawa daga cikin alkawuran da 'yan siyasar kasar suka yi mata ba su cika mata ba.

Dalilin da ya sa na same a gida shi ne saboda ranar Lahadi ne, saboda ranar ce kadai take samun wutu daga wajen aikinta, a yanzu tana aiki ne a matsayin mai akin jinya a wani asibiti mai zaman kansa.

Ta ce min ''Burina shi ne na karanta fannin kimiyya domin na zama likita, to amma iyayena ba su da karfin za su iya daukar nauyin karatuna, a maimakon haka sai na ƙare a ma'aikaciyar jinya''.

Aastha ta nuna min wani kundi da iyayenta suka adana, wanda ya kunshi tarin jaridun da suka yi labarai game da haihuwarta, daga wannan kundi ne ta fahimci abubuwan ban al'ajabi da ke tattare da haihuwarta.

Bayan haihuwarta ta ci gaba ɗaukar hankula, An taɓa gayyatarta wani taron ƙaddamar da shafin yanar gizo na hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar lafiyar ƙasar da hukumar Majalisar Dinkin Duniya na UNFPA, a lokacin tana da shekara 11 da haihuwa.

Aastha ta ce ta fara sanin matsayinta ne bayan da ta fara zuwa makaranta.

''Ina da shekara hudu zuwa biyar lokacin da na fara jin kalmar ni ce mutum na biliyan ɗaya a Indiya a lokacin da 'yan jaridu rike da kyamrori suka zo domin yin hira da ni, a ranar bikin yawan al'umma ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware''.

''Babban al'amari ne ga karamin yaro ya bayyana a gidan talbijin, na kuma ji dadin hakan''.

Yawan labaranta da ake yi ya taimaka mata ta wasu ɓangarorin.

Mahaifinta, wanda mai jiran wani kanti ne, yakan samu akalla dala 50 a wata, kuma da waɗanan 'yan kuɗaɗe yake kudi yake fafutikar biya wa yaransa biyu kuɗin makaranta.

''A duk shekara idan 'yan jarida suka zo domin yin labari a kaina, hakan yana taimaka wajen daga sunan makarantar da nake karatu, wannan ya sa aka yafe min kuɗin makaranta a lokacin da nake aji biyu''.

A makarantar da Aastha ta halarta ta kasance mai ƙoƙari da hazaƙa, ta halarci muhawa da dama da makarantar ta shirya, da gasar rawa, an kuma naɗata muƙamin ɗaya daga cikin shugabannin ɗalibai wato firifet.

A lokacin da take 'yar shekara 16, makarantar ta ba ta kyautar ''daliba mafi ladabi''

Duk da irin ƙwazon Aastha iyayenta sun kasa daukar nauyin karatunta, abin da tilasta mata ficewa daga makarantar zuwa makarantar gwamnati a lokacin da take aji na 11.

''Ban ji daɗin sauyin makarantar ba, kuma abin ya nuna a makina da sakamakon jarrabawa ta, kuma wannan shi ne ƙarshen mafarkina na kasancewa likita''.

Duk da cewa iyayenta talakawa ne, mahaifiyarta ta ce lokaci kaɗan bayan haihuwar Aastha sun yi tunanin cimma duka burukansu.

Iyayenta sun ce Sumitra Mahajan - wato ministar mata da ƙananan yara, a lokacin da aka haifi Aastha - ta yi wa 'yar tasu alƙawarin ɗaukar nauyin karatu da lafiyarta da kudin jirginta a lokacin da ta je barkar haihuwar Aastha a asibitin da aka haifeta a birnin Delhi. To sai dai iyayen nata ba su da wata takarda da ke tabbatar da wannan ikirari nasu.

Mahaifiyar tata ta ƙara da cewa watanni bayan haihuwar Aastha, 'yar majalisar yankinsu ta je gidansu, inda kuma ta tabbatar musu da cewa za ta taimaka wajen sama wa mahifin Aastha aikin gwamnati.

"Mun je ofishinta ya fi sau shurin masaki, amma kullum sai a ce mana ba ta nan, har muka gaji muka hakura'', in ji mahaifiyarta.

Iyayen sun ce taimako ɗaya da suka taɓa samu shi ne na Hukumar Kula da Yawan Al'umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA, wadda ta ba su taimakon rufi 200,000, wato dala 2,425.

Kuɗin da suka ce sun yi amfani da su wajen biya wa yarinyar kuɗin makarantar koyon aikin jinya a lokacin da ta kai shekara 18.

Na kira tsohuwar ministar mata - wadda iyayen Aastha suka ce ta yi musu alƙawarin daukar dawainiyar karatun 'yar tasu, domin jin ta bakinta game da ikrarin na iyayen Aastha.

To sai dai tsohuwar ministar - wadda ta yi ritaya daga harkokin siyasa bayan ta riƙe mukamin kakakin majalisar dokokin kasar - ta ce ba za ta iya tuna wani alkawari da ta yi wa iyayen nata ba, in ban da alƙawarin da hukumar UNFPA ta yi ba.

"Na ziyarce su ne a matsayin na minista ba a kashin kaina ba, daga baya kuma na sauka daga mukamin, na shiga harkokina na siyasa inda na zama 'yar majalisa'' in ji tsohuwar ministar.

Ta ci gaba da cewa iyayen na Aastha ba su tuntuɓe ta ba. ''Idan da a ce sun rubuto min wasiƙa da na taimaka musu, kuma ko da a yanzu ne, suka nemi taimakona zan taimaka musu''.

A 'yan shekarun baya-bayan nan Aastha ta shiga jerin mutanen da ke gangamin rage yawan haihuwa a kasar, inda take bayyana yawan al'umma a matsayin 'matsala' ga ƙasar Indiya

Ta shaida min cewa "dole Indiya ta yi wani abu domin takaita yawan al'ummar ƙasar''.

Ta ƙara da cewa al'adar al'umar ƙasar na son 'ya'ya maza, shi ne ke janyo yawan haihuwa barkatai a ƙasar.

"Idan mutane suka fara haihuwar 'ya'ya mata, sai su yi ta haihuwa har sai sun sami ɗa namiji, saboda sun yi imanin cewa 'ya'ya maza ne kawai za su ɗaga darajarsu''

"Dole gwamnati ta yi wani abu domin sauya wa mutane wanna tunani''

A shekarar 2000, lokacin da aka haifi Aastha, ƙiyasin gwamnatin ƙasar ya nuna cewa zuwa shekarar 2045, yawan al'umar Indiya zai zarta na China.

A watan Yuli, Majalisar Dinkin Duniya ta ce hakan ka iya faruwa a shekara mai zuwa, a yayin da yawan al'umar kasar ya kai biliyan 1.4.

"Gasa na ta ƙaruwa a kowanne ɓangare, mutane da yawa na neman gurbin karatu a makarantu, da wuraren aiki'' in ji Aastha.

"Ni ce mutum na biliyan ɗaya a ƙasarmu, kuma nan ba da jimawa ba za a haifi mutum na biliyan biyu, ina fatan ba za mu kai wannan mataki ba''.