Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta yi wa Madueke farashi, Tottenham na zawarcin Kudus
Chelsea na sa ran samun tayin fiye da fam miliyan 50 kan ɗanwasan gaba na Ingila Noni Madueke mai shekara 23, wanda ya amince ya koma Arsenal. (Telegraph - subscription required)
Tottenham da West Ham na ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar sayen ɗanwasan tsakiya na Ghana Mohammed Kudus, bayan da West Ham ɗin ta yi watsi da tayin farko na fam miliyan 50 da aka yi kan ɗanwasan mai shekara 24. (Sky Sports)
Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Arsenal da ɗanwasan Sporting Viktor Gyokeres mai shekara 27 game da komawarsa ƙungiyar a kan fam miliyan 70. (Record - in Portuguese)
Borussia Dortmund na duba yiwuwar tsawaita kwantiragin ɗanwasan Chelsea mai shekara 21 Carney Chukwuemeka da ke zaman aro a ƙungiyar. (Talksport)
Crystal Palace na dab da sayen ɗanwasan Ajax mai shekara 27 Borna Sosa kan fam miliyan 2. (Athletic - subscription required)
Ana sa ran a ranar Talata Southampton za ta duba lafiyar ɗanwasan Koln Damion Downs. Ɗanwasan Amurka mai shekara 21 zai ƙulla yarjejeniyar shekara huɗu da kulob ɗin. (Florian Plettenberg)
Roma na zawarcin ɗanwasan Brighton da Denmark Matt O'Riley mai shekara 24. (La Gazetta Dello Sport - in Italian)
Ɗanwasan Najeriya Victor Osimhen ya shirya komawa Galatasaray, inda ya yi zaman aro a kakar bara sai dai dole kulob ɗin na Turkiyya ya biya Napoli fam miliyan 65 ganin cewa kulob ɗin bai shirya karɓar ƙasa da haka ba. (Corriere dello Sport - in Italian)
Leeds na ƙyalla ido kan ɗanwasan Hoffenheim Anton Stachs ai dai akwai yiwuwar ta fuskanci gogayya daga wasu ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗanwasan mai shekara 26. (Kicker - in German)
Ɗanwasan Everton mai shekara 35, Idrissa Gueye ya sabunta kwantiragi da kulob ɗin da zai kai shekarar 2027. (Fabrizio Romano)
Daraktan wasanni na Genoa Flavio Ricciardella ya amince da yarjejeniyar sayen Jamie Vardy sai dai kocin ƙungiyar Patrick Vieira ya ƙi amincewa da ɗaukar tsohon ɗanwasan Ingilan wanda ya baro Leicester a makon jiya. (La Repubblica - in Italian, subscription required)
Norwich ta amince ta ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan Denmark mai shekara 23 Mathias Kvistgaarden daga Brondby. (Tipsbladet - in Danish)