Juventus ta zafafa zawarcin Sancho, Rashford zai yi bankwana da Man Utd

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Juventus na ƙara ƙaimi a ƙoƙarin ɗauko ɗanwasan Ingila Jadon Sancho mai shekara 25 daga hannun Manchester United kuma tana iya yin tayin musaya da ɗanwasan Brazil na tsakiya Douglas Luiz mai shekara 27. (Corriere dello Sport - in Italian)

Juventus ɗin kuma na zawarcin ɗanwasan tsakiyar Mali mai shekara 28. Yves Bissouma daga Tottenham Hotspur a wannan bazarar. (La Gazzetta dello Sport - Italian)

Ɗanwasan gaba na Manchester United Marcus Rashford mai shekara 27 da takwaransa na Manchester City Jack Grealish mai shekara 29 na iya samun damar barin ƙungiyoyinsu kan fam miliyan 40 kowannen su a wannan bazarar. (Manchester Evening News)

Barcelona ta shirya tattaunawa da Manchester United a ƴan kwanaki masu zuwa game da yarjejeniyar sayen Rashford a matsayin aro. (Footmercato - in French)

Kocin Paris St-Germain Luis Enrique ya ce ba shi da shakku cewa ɗanwasan Faransa Bradley Barcola zai ci gaba da zama a kulob ɗin duk da zawarcin mai shekara 22 da Bayern Munich ke yi. (Goal)

Al-Nassr ta tattauna da ɗanwasan gaba na Real Madrid Rodrygo mai shekara 24 wanda ƙungiyoyin firimiya da dama ke zawarci. (Sacha Tavolieri - in French)

Tauraruwar tsohon ɗanwasan Italiya Mario Balotelli mai shekara 34 na haskawa a gasar Major League Soccer da Liga MX sakamakon barin Genoa. (Talksport)

Chelsea ta shaida wa Manchester United cewa sai ta biya fam miliyan 35 idan suna son ɗaukan ɗanwasan gaban Faransa Christopher Nkunku mai shekara 27. (Mirror)

Ɗanwasan gaba na Koriya ta Kudu Song Heung-min mai shekara 32 ya shirya ya yi watsi da komawa Los Angeles FC duk da cewa ya bayyana ƙudirinsa na barin Tottenham a wannan bazarar. (Sun)

Sunderland ta yi nisa a tattaunawarta da Club Brugge kan yarjejeniyar sayen ɗanwasa Chemsdine Talbi mai shekara 20, wanda aka haifa a Belgium amma ya zaɓi ya buga wa Morocco. (Sky Sports)

Burnley da Leeds na zawarcin ɗanwasan Amurka da Norwich Josh Sargent mai shekara 25 yayin da wani tayi daga ƙungiyar Wolfsburg ta Jamus bai kai farashin da aka yi masa ba na fam miliyan 16. (Pink Un)

Flamengo ta yi tayin fam miliyan 5 kan ɗanwasan West Brom da Ireland Mikey Johnston mai shekara 26. (Express and Star)

Ɗanwasan Sporting Viktor Gyokeres mai shekara 27 ya ƙi amincewa da tayi daga Saudiyya yayin da yake shirin komawa Arsenal. (Record - in Portuguese)

Sporting za ta kasance cikin shirin amincewa da tsarin biyan Gyokeres albashi bayan da tun asali ta buƙaci euro miliyan 80m, kwatankwacin fam miliyan 69. (A Bola - in Portuguese)