Grealish bai ci wa Man City ƙwallo ba a shekarar 2024

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Jack Grealish bai ci wa Manchester City ƙwallo ba a gabaki ɗayan shekarar 2024.

Rabonda ɗan wasan ya zura ƙwallo a Manchester City tun a Premier League ranar Asabar 16 ga watan Disambar 2023, bayan da suka tashi 2-2 a Etihad.

To sai dai Grealish, wanda tawagar Ingila ba ta je da shi Euro 2024 ba a Jamus, ya ci wa kasarsa ƙwallo biyu a cikin shekarar 2024.

Ya fara ci wa Ingila ƙwallo a Nations League ranar 7 ga watan Satumbar 2024 a karawar da suka doke Ireland 2-0.

Haka kuma Grealish ya zura ƙwallo a raga a wasan da Ingila ta yi nasara 3-1 a gidan Finland ranar Lahadi 13 ga watan Oktoban 2024.

Sau shida ɗan ƙwallon tawagar Ingila ya yi jinya a shekara 2024, wanda ya buga wa Manchester City wasa 18 a shekarar ba tare da zura ƙwallo ba a raga.

A shekarar ya buga Premier League sau 13 da Champions League huɗu da kuma League Cup, duk da haka bai ci ƙwallo ba a 2024.

A farkon shekarar 2024, Grealish ya fara buga gasar Premier ranar Asabar 24 ga watan Agusta, inda City ta doke Ipswich Town 4-1 a Etihad.

Haka kuma wasan karshe da ya yi a 2024, shi ne ranar 21 ga watan Disamba, inda City ta yi rashin nasara 2-1 a Villa Park a hannun Aston Villa.

City ta ci karo da koma baya a bana, wadda ta ci wasa biyu daga karawa 14 da canjaras ɗaya a dukkan fafatawa tun daga 26 ga watan Oktoba da ta doke Southampton 1-0 a Premier League.

Ranar 4 ga watan Janairu, City za ta karɓi bakuncin West Ham a Premier League.

City wadda ta yi karawa 19 a Premier League mai rike da kofi ta ci wasa tara da canjaras huɗu aka doke ta karo shida mai maki 31 tana ta biyar ɗin teburi.