Coventry City ta naɗa Lampard a matsayin kocinta

A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan ne aikin koci na biyar da Lampard ya karba bayan wanda ya yi a Derby, ya ciƙe Chelsea sau biyu sannan Everton.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kungiyar Coventry City ta ɗauki tsohon kocin Chelsea Lampard kan kwantaragin shekara biyu da rabi.

Lampard mai shekara 46 zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar da ke matsayi na 17 a teburi, maki biyu tsakaninta da kungiyoyin da suke ƙasa teburi.

Ya maye gurbin tsohon kocin da ya fi dadewa a ƙungiyar Mark Robins, wanda aka kora daga ƙungiyar a farkon wannan watan bayan shekara bakwai yana jan ragamar ƙungiyar.

Da wannan aikin da Lampard ya zama koci sau biyar a tarihi ba tare da nasara ba, bayan korarsa da aka yi sau biyu a Chelsea da Derby County da Everton.

Ya koma aiki a matsayin mai sharhi kan lamuran wasanni tun bayan korarsa da aka yi daga aiki a matsayin kocin riƙon kwarya a Stamford Bridge a ƙarshen watan Mayun 2023.

Wasan farko da Lampard zai jagoranta shi ne wanda zai yi da Cardiff City a gida a ranar Asabar.

Lampard ya ci yi nasara a wasanni 649 cikin wasa 904 da ya buga a Chelsea, ya ci kofina 11 a shekara 13 a zamansa na Stamford Bridge sannan ya ci kwallo 211 - da haka ya fi kowa yawan cin kwallo a tarhin ƙungiyar.