Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyi 5 da matasa za su bi domin yin kuɗi
A wannan zamani babu wani abu da ke gaban matasa da ya wuce samun rayuwa mai inganci wadda kuma ba za ta samu ba ba tare da samun masu gidan rana ba wato kuɗi ko kuma a ce arziki.
To sai dai da dama daga cikin matasan nan ba su san hanyoyin da ya kamata su bi ba domin samun wannan arziƙi ko kuma kudi da zai huce musu takaicin nasu ba.
Duk da cewa arziƙi ko kuma kuɗi ka iya zama na gado ta yadda matashi zai gaji kuɗi daga wurin mahaifansa ya kuma ci gaba da juya su, amma masana tattalin arziƙi da ƙwararru kan harkokin kuɗi sun yi amannar cewa matasan da ba su gada ba za su iya samun nasarar samun arziƙi a rayuwa.
Dakta Isma'il Muhammad Anchau, babban malami a kwaleji kimiyya da fasaha a Kaduna ya fitar da wasu hanyoyi 5 da matasa za su bi domin samun arziƙi.
"Amma mafi muhimmanci shi ne su mayar da hankali kan ilimi, ƙwarewa, jajircewa da haƙuri, da neman halal domin arziki mai ɗorewa yawanci ba ya zuwa cikin dare ɗaya," in ji Dakta Anchau.
1 - Koyon sana'a
Dakta Isma'ila Muhammad Anchau ya ce da farko ya kamata mutum ya fara duba kansa ya tambayi kansa waɗannan tambayoyi. Wane ne ni? Daga wane tsatso nake? Masu arziƙi ne? Ko kuma talakawa ne? Yaya zurfin ilimina yake?
Dakta ya ce hakan ne zai fara bai wa matashi yanke abin da ya kamata ya yi wajen neman arziƙi.
Dangane da koyon sana'a ko fasaha, Dakta Anchau ya lissafa wasu hanyoyi kamar haka:
- Kwamfuta da fasahar sadarwa (ICT)
- Gyaran waya ko kwamfuta
- Zanen hoto da bidiyo
- Ɗinki, walda, kafinta da sauransu
2 - Kasuwanci
Dangane da kasuwanci wato saye da siyarwa, Dakta Anchau ya lissafa hanyoyin da mutum ya kamata ya bi na kasuwanci kamar haka:
- Saye da sayarwa
- Kasuwancin yanar gizo (online business)
- Dillancin kayayyaki
- Noma ko kiwo a ƙaramin mataki sannan a faɗaɗa
3 - Ilimi da ƙwarewa
Dakta Isma'ila Muhammad Anchau ya ƙara da cewa matasa masu ilimi na da banbanci da masu ƙarancinsa kasancewar ilimi zai bayar da damar samun ƙwarewa a fannoni daban-daban na zamani. Ya kuma lissafa hanyoyin ƙwarewa kamar haka:
- Koyon shirye-shiryen kwamfuta (programming)
- Kasuwancin intanet (Digital marketing)
- Ƙirƙirar shirye-shirye a kafafen sadarwa (Content creation)
- Zayyana (Graphic design)
- Ƙwarewa kan alƙaluma (Data analysis)
4 - Ajiya da zuba jari
Dakta Anchau ya ce akwai hanyoyi guda biyu na zuba jari da ajiya da duk wanda aka bi ka iya kai mutum ga samun arziƙi:
- Adana wani kaso na kudin shiga akai-akai
- Zuba jari cikin halastattun hanyoyi bayan samun ilimi a kai
5 - Gina kyakkyawar alaƙa da mutane
Babban malamin na kwalejin fasaha ta Kaduna ya ce ƙari a kan waɗancan hanyoyin guda hudu na neman arziƙi akwai kuma buƙatar mutum ya yi ƙoƙari wajen gina kyakkyawar alaƙa da sanayya da mutane.
- Sadarwa da manyan masu kasuwanci
- Halartar tarukan koyarwa da ci gaban sana'a
- Neman masu ba da shawara
Dakta Anchau ya ƙara da jan hankalin matasa da ma duk masu neman arziƙi da su tabbatar da cewa duk sana'ar da za su yi su guji abubuwa kamar haka:
- Son samun kuɗi cikin gaggawa ba tare da aiki ba.
- Damfara ko hanyoyin samun kuɗi marasa gaskiya.
- Kashe kuɗi fiye da yadda ake samu.
- Sakaci da ilimi ko koyon sabbin dabaru.