Ana zanga-zanga a Isra'ila gabanin yin sauye-sauye kan ɓangaren shari'ar ƙasar

Isra'ila

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ƴan sanda sun yi amfani feshin ruwa kan masu zanga-zanga da suka toshe wata babbar hanya kusa da birnin Kudus
An wallafa

Dubun-dubatar masu zanga-zanga sun toshe hanyoyi a faɗin Isra'ila, da kuma yin alwashin bijire wa shirn gwamnati na kawo sauye-sauye a ɓangaren shari'ar ƙasar.

Ƴan sanda sun yi amfani da mesar ruwa domin tarwatsa masu zanga-zanga a kan titunan birnin Tel Aviv, inda aka kama mutane 42 kawo yanzu.

Hakan na zuwa ne bayan da wani kuduri na rage wa Kotun Kolin Ƙasar karfi kan matakin da ministoci ke ɗauka ya wuce karatu na biyu a gaban majalisa a ranar Litinin da dare.

Shirin kawo sauye-sauyen ya gurgunta harkoki a ƙasar, abin da kuma ya janyo gagarumar zanga-zanga.

A wani abu mai kama da wasan kwaikwayo a ginin majalisa a birnin Kudus jim kaɗan kafin ƴan majalisa su kaɗa kuri'a kan kudurin, masu zanga-zanga sun yi kokarin kutsawa cikin ginin majalisar kafin jami'an tsaro su tarwasa su.

Kudurin na cikin wani ɓangare na sauye-sauye da ake shirin yi na rage wa ɓangaren shari'a karfi wanda gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu ta kawo, wadda ta kasance mafi tsattsaurar ra'ayi a tarihin Isra'ila.

Ta bayyana cewa kotuna suna da karfi fiye da kima a ɓangaren siyasa, wanda ya saɓa da zaɓin masu kaɗa kuri'a.

Masu sukar sauye-sauyen sun ce shirin da gwamnati ke yi na da girman gaske kuma barazana ce ga tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.

Jagororin masu zanga-zanga sun yi kira da ranar nuna turjiya a ranar Talata ko da kudurin da aka kawo gaban majalisa a daren Litinin zai iya wuce karatu na farko cikin uku da ake buƙata kafin ya zama doka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An fara boren ne a safiyar ranar Talata, inda masu zanga-zangar ke ɗaga tutoci da buga ganguna da kunna wuta da kuma rera take daban-daban yayin da suka tsohe hanyoyi a faɗin ƙasar, abin da ya janyo cunkoson ababen hawa.

A garin Herzliya da ke arewacin Tel Aviv, masu zanga-zanga sun ƙona tayoyi a tsakiyar wata hanya kafin ƴan sanda su cire su daga kan titin.

A ɗaya ɓangare kuwa, wasu ƴan mazan jiya sun gudanar da zanga-zanga a filin jirgin sama na Ben Gurion.

Ana sa ran cewa za a samu ƙarin mutane da za su fito zanga-zanga a filin jirgin da kuma a wajen gidan shugaban ƙasar a birnin Kudus wato a ma'aikatar tsaron ƙasar da ke Tel Aviv da kuma reshen ofishin jakadancin Amurka.

Sauyin mai cike da ce-ce-ku-ce ya raba kan ƙasar, inda zanga-zangar da ake gudanarwa kowane mako - ke tara dubban mutane kan tituna - tun bayan da gwamnati ta bayyana aniyarta na yin sauyin a farkon wannan shekara.

Haka nan ma, ɗaruruwan sojojin ƙasar - sun yi barazanar daina fitowa bakin aiki lokacin da ake zanga-zanga.

A ranar Talata ne wasu sojojin da jami'an leƙen asiri na Mossad su ma suka bi bayan sauran sojojin da suka yi barazanar daina fitowa aiki.

Shugaban ma'aikata na rundunar sojin ƙasar ya ce sojojin da ke taimakawa, suna da damar kin fita wajen aiki, kuma sojojin sun ce za su ɗauki mataki kan kowane jami'i da ya ki fitowa bakin aiki.