Man United na shirin cefanar da Lindelof, kungiyoyin saudiyya na son golan Man City

An wallafa

Ana neman golan Manchester City Ederson a Saudiyya, Manchester United na son siyar da Victor Lindelof kuma za ta iya zawarcin Ivan Toney da dai sauransu.

Manchester City ta karbi tayin fan miliyan 25 daga Saudiyya kan golanta dan kasar Brazil Ederson mai shekaru 30. (HITC)

Manchester United na son siyar da dan wasan bayan Sweden Victor Lindelof, mai shekara 29, a bazarar nan kuma za ta saurari tayin dan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen mai shekaru 32. (Manchester Evening News)

Chelsea a shirye take don yin takara da Tottenham, da Bayern Munich da Paris St-Germain kan dan wasan Rennes dan kasar Faransa Desire Doue, mai shekara 19. (L'Equipe French)

Manchester United na zawarcin dan wasan Brentford da Ingila Ivan Toney, mai shekara 28, wanda ke shirye ya koma Old Trafford. (Christian Falk)

Kulob din Seria A Como na shirin dauko dan wasan bayan Faransa Raphael Varane, mai shekara 31, a kyauta bayan ya bar Manchester United a bazara. (Fabrizio Romano)

West Ham ta nuna sha'awarta ta neman dan wasan gaban Netherlands Steven Bergwijn, mai shekara 26, amma Marseille da wasu kungiyoyin Saudi Arabiya suma suna fatan zawarcinsa daga Ajax. (De Telegraaf)

Ana sa ran Atletico Madrid za ta bai wa AC Milan damar sayen Alvaro Morata, mai shekara 31, mako mai zuwa bayan wasanda kasarsa za ta yi na wasan karshe na gasar cin kofin Turai (Calciomercato Italian)

Everton, West Ham da Newcastle na shirin rasa Federico Gatti, mai shekara 26, yayin da mai tsaron bayan dan Italiya ke son komawa uventus. (Tuttosport)

Dan wasan bayan Portugal Nuno Tavares, mai shekara 24, yana gab da komawa Lazio a matsayin aro daga Arsenal. (Fabrizio Romano)

Dan wasan Faransa Allan Saint-Maximin, mai shekara 27, na shirin barin Al-Ahli domin kulla alaka da Jose Mourinho a Fenerbahce. (Yagız Sabuncuoglu)

Arsenal da Manchester United da Aston Villa suna zawarcin dan wasan Girona da Ukraine Viktor Tsygankov mai shekara 26. (AS Spanis)

Nottingham Forest ta fara tattaunawa da Fiorentina kan dan wasan bayan Serbia Nikola Milenkovic mai shekara 26. (Gianluca di Marzio)

Leicester ta shirya tayin £21.5m don siyan dan wasan gaban Juventus dan kasar Argentina Matias Soule, mai shekara 21. (La Gazzetta dello Sport}