Man Utd za ta samu damar sayen Olise, Zubimendi ya sa Arsenal raba ƙafa

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta samu damar sayen dan wasan gaba na gefe na Crystal Palace Michael Olise, na Faransa mai shekara 22, a bazara. (90min)
Haka kuma Manchester United din tana da kwarin gwiwa tayin tsakanin fam miliyan 60 zuwa 70 zai iya ba ta damar sayen dan bayan Everton Jarrad Branthwaite, dan Ingila mai shekara 21, kafin ranar 30 ga watan Yuni, abin da zai bai wa Everton damar sanya kudin a cikin asusunta na kakar 2023-24 domin kauce wa kara zaftare mata maki. (Football Insider)
An sheda wa Arsenal da Manchester City cewa Newcastle United za ta saurari tayin da ya wuce fam miliyan 80 a kan dan wasanta na tsakiya Bruno Guimaraes, na Brazil a bazaran nan. (90min)
Damar sayen Guimaraes a kan fam miliyan 100 za ta iya amfani ne tsawon wata daya kawai daga karshe-karshen watan Mayu zuwa karshen watan Yuni. (Fabrizio Romano, daga Caught Offside)
Watakila Manchester United ta nemi sayen dan bayan Girona Miguel Gutierrez dan Sifaniya mai shekara 22, amma kuma za ta iya fuskantar gogayya daga Arsenal da West Ham. (GiveMeSport)
Arsenal na zawarcin 'yan wasan tsakiya da dama saboda ganin tunanin cewa cinikin dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Sifaniya Martin Zubimendi, mai shekara 25, zai iya zama da wuya. (Standard)
Zubimendi ya ce rahotannin da ke alakanta shi da wasu manyan kungiyoyi na Turai shaci-fadi ne kawai saboda ya ce shi yana jin dadin zamansa a Real Sociedad. (Marca)
Manchester United za ta nemi sabon babban dan baya da kuma babban dan wasan tsakiya a bazara, kuma Anthony Martial, ba ya daga cikin 'yan wasan da za ta yi amfani da su a nan gaba. (Football Insider)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Watakila kociyan Wolves Gary O'Neil ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar duk kuwa da rahotannin da ke alakanta shi da aikin Liverpool. (GiveMeSport)
Ajax na sha'awar aikin tsohon kociyan Chelsea da Brighton Graham Potter, wanda kuma Manchester United ke sanya shi a jerin wadanda za ta zaba domin maye gurbin Erik ten Hag. (Guardian)
Potter ya yi watsi da tayin farko na Ajax saboda albashin da kungiyar ta ce za ta ba shi bai yi masa ba. (Het Parool)
Manchester United, da Paris St-Germain da kuma Bayern Munich, dukkanninsu suna son mai tsaron ragar Real Madrid Andriy Lunin, dan Ukraine. (Fichajes)
Kanada ta tuntubi tsohon kociyan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer da kuma tsohon kociyan Leeds United Jesse Marsch domin zama kociyan tawagar kasar zuwa gasar kofin dunita ta 2026. (Standard)
Napoli ta bi sahun kungiyoyin da ke son sayendan gaban Kanada Jonathan David, daga Lille. (Calciomercato)
A shirye kungiyar gasar Jamus, Stuttgart take ta sayi dan gaban Brighton Deniz Undav, na Jamus bayan da ta karbi aronsa a bazarar da ta gabata. (Caught Offside)











