Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta caskara Osasuna a La Liga
Real Madrid ta caskara Osasuna da cin 4-0 a wasan mako na 12 da suka kara a La Liga ranar Asabar a Santiago Bernabeu.
Vinicius Junior ne ya ci uku rigis da kuma Jude Bellingham da ya zura ɗaya a raga a wasan na babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
To sai dai duk da nasarar da Real ta yi, ta ci karo da samun masu rauni a ƙungiyar, inda Rodrygo ya fita daga karawar bayan minti na 20, yayin da Lucas Vazquez bai koma zagaye na biyu ba.
A watan jiya ne Dani Carjaval ya ji rauni, inda har yanzu David Alaba ke jinya.
Da wannan sakamakon Real Madrid wadda take ta biyu a teburin La Liga ta rage tazararta da Barcelona ta ɗaya zuwa maki shida.
To sai dai kuma watakila ƙungiyar da Hansi Flick ke jan ragama ta sake bai wa Real tazarar maki tara da zarar ta doke Real Sociedad ranar Lahadi.
Real Madrid mai kwantan wasa da Valencia ta yi rashin nasara 4-0 a gida a hannun Barcelona a El Clasico ranar Asabar 26 ga watan Oktoba.
Daga nan Real ta yi rashin nasara ta biyu a jere, bayan da AC Milan ta je ta doke 3-1 a Champions League ranar Talata 5 ga watan Nuwamba.
Ranar Lahadi 24 ga watan Nuwamba, Real Madrid za ta je gidan Leganes a wasan mako na 13 a La Liga.