Barca ta saka ƴan wasa uku masu shekara 17 a tare a La Liga

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta fara kakar 2023/24 da kafar dama, bayan da ta je ta doke Valencia 2-1 ranar Asabar a wasan makon farko a La Liga.

To sai dai ƙungiyar ta yi amfani da matasa uku masu shekara 17 a karawar da ta je ta ci Valencia.

Cikinsu sun haɗa da Lamine Yamal da Cubarsí da kuma Marc Bernal, waɗanda aka fara fafatawar da su.

Karo na biyu da Barcelona ta yi amfani da ƴan ƙwallo uku a lokaci ɗaya masu kasa da shekara 18.

Haka kuma Barcelona ce keda wannan tarihin a karni na 21 ta kuma kara maimaita hakan a bana.

Ta fara yin hakan a Mayun 2024 lokacin da Xavi ke koci, wanda ya fara da Lamine Yamal da Cubarsí da kuma Hector Fort a karawa da Almeria.

Hansi Flick shi ne ke horar da Barcelona, bayan da ƙungiyar ta raba gari da Xavi a bara.

Barcelona na fama da matsin tattalin arzikin da take tsuke bakin aljihu, sannan tana kokarin bin dokar La Liga ta kashe kuɗi daidai samu.

A kakar nan ta bana Barcelona ta sanar da cewar ƙyaftin ɗinta, Sergi Roberto ya bar ƙungiyar.

Haka kuma ta sayar da Marc Guiu ga Chelsea a cikin watan Yuli da kuma Julian Araujo da ya koma Bournemouth cikin watan Agusta.

Ita kuma ta ɗauki Dani Olmo ranar 9 ga watan Agusta daga RB Leipzig.

A kakar da ta wuce Barcelona ta kare a mataki na biyu a teburin La Liga, inda Real Madrid ta lashe kofin tare da na Champions League.

Ranar Asabar Barcelona za ta karɓi bakuncin Athletic Bilbao a wasan mako na biyu a La Liga.