Liverpool za ta saida Diaz, Man U za ta yi musayar 'yan wasanta Rashford da Pavlovic

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool za ta saida dan wasan gaba na Colombia mai taka ma ta leda, Luis Diaz, 28, a kakar nan domin samun isassun kudin da za ta sayi mai cin kwallo a kungiyar. (Football Insider)

Da alama an kure hakurin kungiyar hakurin Manchester City, inda ta dauki matakin sauya 'yan wasan da ba sa amfana ma ta komai sakomakon raunin da suka ji ko gajiyawa. Wannan matakin zai sanya makomar 'yan wasa irin dan wasan tsakiyar Belgium Kevin de Bruyne, 33, da dan wasan Ingila John Stones, 30. (Guardian)

Arsenal ta sake nuna sha'awar dauko dan wasan Juventus Dusan Vlahovic, 25, inda kuluf din na Sabiya zai saida dan wasan kan farashi mai rahusa na fam miliyan 33. (CaughtOffside)

Manchester United, Liverpool da Chelsea na son yin ram dan wasan Faransa Castello Lukeba, da akai wa farashin fam miliyan 74.5 (Daily Briefing by Christian Falk )

West Ham ta sabunta aniyarta na dauko dan wasan Canada mai taka leda a Jonathan David, 25, wanda ke shirye domin komawa wata kungiyar a kakar nan. (Guardian)

Manchester United ka iya samun rarar miliyoyin kudi idan suka amince da dauko tsohon dan wasan kungiyar Angel Gomes, 24, daga Lille, inda dan wasan tsakiyar na Ingila ke kasuwa a kakar nan. (Manchester Evening News),

Golan Royal Antwerp's Belgian, Senne Lammens, 22, ya sha mamakin yadda ake yada jita-jitar wai zai koma kungiyar Manchester United. (90min).

Manchester United na duba yiwuwar yarjejeniyar da za ta ba dan wasan Ingila Marcus Rashford, 27, damar koma wa Bayern Munich, ya yin da mai tsaron baya na Jamus Aleksandar Pavlovic, 20, ya koma Old Trafford da taka leda. (CaughtOffside)