Chelsea za ta rabu da Mudryk, Arsenal na tattaunawa da Magalhaes

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A shirye Chelsea take ta bar ɗan wasanta na gaba na gefe Mykhailo Mudryk ya tafi a watan Janairu, kuma Marseille na son ɗan wasan na Ukraine mai shekara 23. (Teamtalk)

Arsenal ta fara tattaunawar kwantiragi da ɗan bayanta Gabriel Magalhaes, ko da yake tattaunawar da ɗan wasan na Brazil ta farko-farko ce ba ta yi nisa ba. (Football Insider)

An bayar da rahotannin cewa Christian Eriksen zai bar Manchester United a bazara, to amma ɗan wasan na Denamark wanda yake da sauran shekara ɗaya a kwantiraginsa, ya ce ba ya tunanin barin ƙungiyar ta Old Trafford. (Mail)

Mai ba wa AC Milan shawara, Zlatan Ibrahimovic ya tuntuɓi tsohon kociyan Borussia Dortmund Edin Terzic, kasancewar kociyan ƙungiyar ta Serie A Paulo Fonseca - wanda aka naɗa a bazara - yana shan matsin lamba bayan da ya fara kakar nan ba tare da wani ƙwazo ba. (Sky Sports)

Shugaban Inter Milan Guiseppe Marotta ya ce, ƙungiyar na dab da sayen ɗan wasan Manchester City da Norway, Erling Haaland, mai shekara 24, a lokacin yana ɗan shekara 15, sai kawai aka samu tangarɗa sakamakon batu na dogon-Turanci ko wasu ƙa'idoji. (Football Italia)

Har yanzu ana sa ran Ben Chilwell zai bar Chelsea a watan Janairu, duk da cewa ɗan wasan ya koma atisaye da tawagar manyan ƴan wasan ƙungiyar, bayan da ya kasa samun tafiya a bazara. (Football Insider)

Chelsea za ta iya naɗa Sachin Gupta, wanda mataimakin shugaban ayyuka ne na ƙungiyar wasan ƙwallon kwando ta Minnesota Timberwolves, da ke Amurka, a wani matsayi a ƙungiyar ta Stamford Bridge. (Athletic)

Newcastle United na sa ido a kan matashin ɗan bayan Chelsea Josh Acheampong mai shekara 18, kuma za ta iya neman sayen ɗan wasan na tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 19. (i newspaper)