Roma ta kori Rossi bayan wasa huɗu da ya ja ragama a bana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Roma ta kori kociyanta, Daniele de Rossi bayan wasa huɗu da ya ja ragama a Serie A a kakar bana.

Roma, ta ɗauki De Rossi ya maye gurbin Jose Mourinho a Olimpico a Janairu, bai ci wasa ko ɗaya ba a Serie A a kakar nan, ya yi canjarras uku da rashin nasara ɗaya.

Roma tana mataki na 16 a teburin Serie A, bayan da ta tashi 1-1 a Genoa ranar Lahadi.

De Rossi ya fara kakar bara da kafar dama, a wasa 11 a Roma ya yi rashin nasara ɗaya da haɗa maki 26 daga 33 da ya kamata ya samu, inda Roma ta kare a mataki na biyar daga na tara da ya karɓi ƙungiyar.

Ta kuma kai matakin daf da karshe a Europa League daga baya Bayern Leverkusen ta yi waje da ita a gasar.

Bayan da ta kare a mataki na shida a kan teburi a bara, ta samu tikitin shiga Europa a bana.

A kakar nan Roma ta ɗauki Artem Dovbyk daga Girona da ɗan wasan tawagar Jamus, Mats Hummels.

Wasu daga cikin ƴan wasan da suka bar Roma kan fara kakar bana sun haɗa da Chris Smalling da ya koma Al-Fayha ta Saudi Arabi da Tammy Abraham zuwa AC Milan da zai yi wasannin aro da kuma Romelu Lukau da ya koma Napoli.

Haka kuma Andrea Belotti ya koma Como da Rui Patricio zuwa Atalanta da kuma Leonardo Spinazzola zuwa Napoli.

De Rossi a matakin ɗan wasa, wanda yake da shekara 41 da haihuwa, ya yi kaka 22 a Roma tsakanin 1997 zuwa 2019 da buga wasa 616.

Yana cikin tawagar Italiya da ta lashe kofin duniya a 2006.