Dalilin da ya sa dole Man United ta kama da kyau a wasa da Bilbao

'Yanwasan Man United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yanwasan Man United Casemiro da Dallot kenan suke murna a wasansu da suka doke Lyon
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United za ta je Sifaniya a yammacin yau a matsayin abin tausayi.

Ita ce ta 14 a teburin Premier League, yayin da Athletic Bilbao take ta huɗu a gasar La Liga ta Sifaniya.

Sai dai kuma, United ta saba yunƙurowa domin ceto kakar wasan da ta ba ta yi ƙoƙari ba daga ƙarshe - kamar kofin FA na kakar bara, wanda ba a taɓa tsammanin za ta doke Man City ba.

Ba don wannan nasarar lashe FA Cup ba da Man United ba ta zo gasar Europa ta bana ba gaba ɗaya, yanzu kuma suke da damar zuwa Champions League idan suka ci Europa.

Abu ne mai wuya a iya amincewa da shi ganin yadda ta yi rashin nasara a wasa 15 na Premier League a bana.

Ƙarfin da Bilbao ke da shi na da tsoratarwa, amma kuma dole ne United ta ƙudurce cewa za ta iya yin nasara.

A kaka mai zuwa, mai horarwa Ruben Amorim zai zama cikin matsi domin inganta al'amuran ƙungiyar bayan abin kunya lokacin da ya zo. Idan United ta ci gaba da rashin nasara a watannin farko na kakar, aikinsa zai iya gamuwa da cikas.

Lashe Europa zai taimaka sosai. Haka nan, samun gurbin Champions League kuma zai sa ya samu ƙarin kuɗin sayen 'yanwasa domin ƙarfafa ikonsa.

Wani dalilin da zai sa United ta ji kamar za ta iya shi ne, ita kaɗai ce ba a doke ba cikin duka gasar zakarun Turai uku a wannan kakar bayan wasa 12.

Abin da zai kai su Sifaniya kenan. Su guji rashin nasara kuma su ƙarasa aikin a Old Trafford - kamar yadda suka yi wa Real Scieded da Lyon.