Rashford zai rage albashi don komawa Barca, Madrid ta bi sahun masu neman Duran

Asalin hoton, Getty Images
Marcus Rashford na shirin amincewa da rage masa albashi don komawa Barcelona daga Manchester United, Real Madrid ta zama kungiya ta baya-bayan nan da ta nuna sha'awar daukar dan wasan gaban Aston Villa Jhon Duran, Newcastle United na shirin sabunta kwantiragi na dogon lokaci ga Alexander Isak.
Dan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 27, a shirye yake a rage masa albashi a kokarinsa na komawa Barcelona a watan Janairu. (Daily Star)
Za a iya taimakawa Barcelona wajen siyan dan wasan Ingila Rashford idan dan wasan bayan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 28, ya bar kungiyar. (Mundo Deportivo)
Manchester United ta nemi a sanar da ita makomar dan wasan gaban Chelsea da Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 27 (ESPN)
Daraktan Napoli Giovanni Manna ya tabbatar da cewa kungiyar na zawarcin Garnacho da dan wasan gaban Borussia Dortmund na kasar Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 23 (Football Italia)
Newcastle United na shirin ba wa dan wasan gaban Sweden Alexander Isak, mai shekara 25 sabon kwantiragi na dogon lokaci a bazara. (Sunday Telegraph)
Real Madrid ta bi sahun Paris St-Germain da Al-Nassr wajen neman dan wasan Aston Villa da Colombia Jhon Duran mai shekaru 21. (Footmercato French)
Dan wasan gaba na Slovenia Benjamin Sesko zai fi son komawa Arsenal a kan Chelsea ko Manchester United amma RB Leipzig ba ta son siyar da dan wasan mai shekaru 21 a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (Talksport)
Bayer Leverkusen na zawarcin dan wasan tsakiyar Aston Villa Emiliano Buendia. Kulob din na Jamus yana neman lamuni tare da zabin siyan dan wasan Argentina mai shekaru 28 (Sky Sport Germany)
Kocin Fenerbahce Jose Mourinho na son dauko dan wasan Barcelona dan kasar Sipaniya Ansu Fati, mai shekara 22, a matsayin aro domin bunkasa kungiyarsa ta lashe gasar. (AS Spanish)
Chelsea ta amince da tayin Yuro miliyan 12 daga Lazio kan dan wasan tsakiyar Italiya Cesare Casadei, mai shekara 22, a yarjejeniyar da ta kunshi kashi 25% na cinikin. (Sport Italy)
Ana alakanta dan wasan gaban Lyon da Algeria Said Benrahma, mai shekara 29 da Ipswich amma yana tattaunawa kan komawa Neom SC, wadda ke mataki na biyu a gasar Saudi Arabiya. (Footmercato French)











