Wataƙila Rashford zai yi jinya har bayan kakar nan

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Marcus Rashford, wanda ke buga wasannin aro a Aston Villa daga Manchester United, zai yi jinya har karshen kakar nan.
Har yanzu ana auna girman raunin da ɗan wasan tawagar Ingila ya ji, wanda ya hana shi buga daf da karshe a FA Cup da Crystal Palace ta ci 3-0 ranar Asabar.
Sai dai ana ganin da ƙyar idan matashin mai shekara 27, zai sake komawa taka leda kafin a karkare gasar Premier League ta bana.
Abin da ke gabansa shi ne yadda zai murmure da wuri kafin watan Yuni, domin buga wa Ingila wasan neman shiga gasar kofin duniya da za ta yi da Andorra da wasan sada zumunta da Senegal.
Idan kuma zai warke kafin kammala Premier League, sai dai ya fuskanci Tottenham ranar 18 ga watan Mayu.
Ba damar ya buga wasan karshe da Villa za ta karɓi bakuncin Manchester United a Premier League ranar Lahadi 25 ga watan Mayu a Villa Park.
Ranar Asabar, Rashford ya je ya kalli kayatatcen damben boksin tsakanin Chris Eubank Jr da Conor Benn da aka yi a filin wasa na Tottenham.
Har yanzu Rashford bai ce komai ba kan makomarsa, wanda sai an kammala kakar nan zai yi karin bayani.
Yarjejeniyar Rashford za ta kare a karshen kakar 2028, amma baya jin zai kara taka leda karkashin Ruben Amorim da zarar ya koma Old Trafford.
Thomas Tuchel ya gayyaci Rashford cikin tawagar Ingila a watan Maris, wanda bai buga Euro 2024 ba.











