Da wuya Alisson ya iya buga wasan Liverpool da Bournemouth

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Liverpool Arne Slot ya ce ana kokwanton ko mai tsaron gida Alisson Becker zai iya fuskantar Bournemouth a wasan Premier na ranar Asabar saboda rauni da ya ke fama da shi.
Alisson ya buga dukkan wasanni huɗu da ƙungiyar ta Anfield ta buga a gasar bana, kuma ya buga wasa da AC Milan a gasar zakarun Turai ranar Talata.
Haka kuma ya buga wa Brazil wasanni a gasar Copa America a lokacin bazara da kuma lokacin hutun wasannin ƙasa da ƙasa na baya-bayan nan.
Da aka tambaye shi batun yawan wasannin da ake bugawa kowace shakara ɗan wasan mai shekaru 31 ya ce "babu wanda ya ke tambayar ƴan wasan game da yawan aikin da suke yi.''
"Ba lallai ne Alisson ya iya atisaye ba." in ji Slot. ''Sai dai mu sanya ido mu gani.''
Ba a ga Alisson a atisayen ƙungiyar na ranar Juma'a ba, inda Caoimhin Kelleher da Vitezslav Jaros ne suka kasance a raga.
Kelleher ne ya maye gurbin Alisson a lokacin da ɗan wasan na Brazil, ya shafe fiye da watanni biyu yana jinya a kakar da ta gabata.
Liverpool za ta karɓi baƙuncin Bournemouth ranar asabar a wasanta na uku cikin guda bakwai da za ta buga cikin kwanaki 22.










