Ko masu zaɓen Amurka a ƙasashen waje za su iya sauya alƙiblar sakamakonsa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Zaɓen shugaban ƙasar na ranar 5 ga watan Nuwamba na nuna alamamun kankankan a tsakanin 'yan takarar - ana ma ganin kusan shi ne wanda zai fi kasancewa kankankan a tarihin ƙasar.
Da hasashen da ake yi na samun ƙaramar tazara ta ƙuri'u a tsakanin Donald Trump na Republican da kuma Kamala Harris ta Democrat, a manyan jihohi da dama, ana ganin ƙuri'ar Amurkawa da ke ƙasashen waje za ta yi matuƙar tasiri.
Kusan ƴan Amurka da suka wuce shekara 18 da haihuwa miliyan uku da ko dai suke zaune dindindin ko kuma suke zaune zaman wucin-gadi a waje suka cancanci kaɗa ƙuri'a, kamar yadda hukumomin ƙasar suka yi ƙiyasi.
Waɗannan Amurkawan sun kama daga sojoji da jami'an diflomasiyya da iyalansu da 'yan cirani da ɗalibai.
Daga cikinsu akwai Katie Benson – wadda tun tana shekara 12 da ke shirya yadda za ta yi zaɓen.
A zaɓen 2016 ita da mahaifiyarta sun kwanta bacci da fatan su tashi da safe su ji Hillary Clinton ta zama mace ta farko da ta zama shugabar ƙasar Amurka.
Ta ce, abin da dugunzuma ta, da ta tashi da safe ta ji cewa burin Hillary Clinton bai tabbata ba kuma Mista Trump ya yi nasara a zaben da ya kasance mafi taƙaddama da sarƙaƙiya a tarihin Amurka.
Ta ce wannan zaɓe ya sa ta farka a kan siyasar Amurka. Ya sa har kullum take so a ce wata rana ta zo da za ta taka muhimmiyar rawa a zaɓen, in ji ɗalibar wadda ke karatu a jami'ar Cambridge a Birtaniya.

Asalin hoton, Getty Images
An haifi Ms Benson a Birtaniya amma kuma tana da fasfon Amurka. Wadda a yanzu take 20, ta taɓa yin zaɓe a karon a zaɓen shugaban ƙasa na Amurka ta hanyar aikawa da ƙuri'arta ta wasiƙa a ƙarshe-ƙarshen watan Satumba.
Ta ce, ''ina jin wani nauyi ne da ya rataya a wuyana na yi zaɓen ba domin kaina ba kawai domin sama wa Amurka makoma ta gari.''
Dangin mahaifiyarta da take ziyara a kai-a kai suna zaune ne a jihar Wisconsin, wadda ta kasance ɗaya daga cikin jihohi bakwai da za su tantance wanda zai ci zaɓen - jihohin ba-a-san-maci-tuwo-ba - Arizona, da Georgia, da Michigan, da Nevada, da North Carolina da kuma Pennsylvania.
Amurkawa da ke waje suna kaɗa ƙuri'arsu ne ta jihohin da su ko danginsu suka yi rijista ta ƙarshe - saboda haka Ms Benson a yanzu ƙuri'arta za ta kasance ne a Wisconsin.
Tazara mai girma
A tsarin zaɓen Amurka mai sarƙaƙiya, shugaban ƙasa ba ya samun nasara da mafi yawan ƙuri'un jama'a, sai ta hanyar yawan jihohin da ya ci.
Ana zartar da wanda ya ci zaɓen ne ta hanyar wakilan jihohi inda kowace jiha take da yawan wakilai daidai da yawan jama'arta.
A kowace jiha ɗantakarar da ya fi yawan ƙuri'a daga jama'a ya samu dukkanin ƙuri'ar wakilan jihar.
Ɗantakarar da ya samu 270 ko fiye da haka daga cikin jimillar wakilai 538 shi ne zai zama shugaban ƙasar.

A fili take a tarihi da kuma yanayin kaɗa ƙuri'u inda yawancin jihohi 50 na Amurka za su karkata a zaɓen, to amma jihohin ba-a-san-maci-tuwo ba ka iya karkata kowane ɓangare.
Kwamitin zartarwa na jam'iyyar Democrat ya yi ƙiyasin cewa 'yan Amurka miliyan 1.6 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen daga waɗannan jihohi daga ƙasashen waje.
To amma kuma idan ana maganar tsagwaron yawan masu zaɓe ne to a iya cewa masu zaɓen na waje ba su taka kara sun karya ba.
Daga cikin ƙuri'a sama da miliyan 161 da aka jefa a zaɓen shugaban ƙasa na 2020, ƙasa da 900,00 daga waje.
Amma kuma duk da haka tun da batu ake na yawan ƙuri'u akwai yanayin da za a iya samu da ƙuri'un na Amurkawa da ke ƙasashen waje za su iya taimaka wa ɗan takara ya yi nasarsa.
Dambarwar Bush da Gore ta Florida
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
“Wannan rukunin na masu zaɓe ya nuna gagarumin tasirin da yake da shi na tasiri a zaɓuka, duk da cewa bambancin da ake da shi a siyasarmu da ta rabu kusan kankankan yake," in ji Farfesa Jay Sexton, darektan cibiyar dumukuraɗiyya a jami'ar Missouri da ke Amurka (Kinder Institute on Constitutional Democracy).
Ɗaya daga cikin fitaccen babban misali a nan shi ne - dambarwar zaɓen shugaban ƙasa na 2000 tsakanin George W Bush na jam'iyyar Republican da kuma Al Gore na Democrat, ina sakamakon ƙarshe ya dogara ga ƙuri'un jihar Florida da ke kankankan.
Bayan dambarwa sake ƙirge da shari'a da aka yi ta yi a ƙarshe dai Kotun Ƙolin Amurka ta zartar cewa Mista Bush ne ya yi nasara - a Florida - kuma hakan ya sa ya zama wanda ya yi nasara a zaɓen Amurkar - da bambancin ƙuri'a 537 kawai.
Yayin da ake ta sake ƙirga ƙuri'un, haka ma kuma ƙuri'un masu zaɓe da ke ƙasashen waje ke ta zuwa - kuma ana ta dambarwa kan ko za a soke wasu ƙuri'un bisa dalilin rashin sanya bayanan aikewa da wasiƙa daidai ko kuma rashin zuwa a kan lokaci.

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Sexton ya ce, bisa bayanan alƙaluman ma'aikatar harkokin wajen Florida, idan ba don waɗannan ƙuri'u na waje ba da aka ƙirga bayan zaɓe da Mista Gore ne zai yi nasara a jihar da bambancin ƙuri'u 202.
A 2020, ɗan takarar jam'iyyar Democrat a lokacin -shugaban ƙasa na yanzu -Joe Biden ya bayar da mamaki, inda ya samu nasara da bambancin yawan ƙuri'u kaɗan a kan Trump a jihohi biyu da a tarihi na jam'iyyar Republican ne - Georgia da Arizona.
Bayanai sun nuna yadda ƙuri'un Amurkawa masu zaɓe da ke ƙasashen waje suka yi tasiri a nan, in ji Sharon Manitta, mai yi wa jam'iyyar Democrat yaƙin neman zaɓe a waje.

Asalin hoton, Getty Images
"Muna ƙokarin mu tarad da su,” in ji Greg Swenson, shugaban babbar ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Republican reshen Birtaniya.
Ya ce ƙungiyar na neman mayar da hankali a kan sansanonin soji. Yawanci ana ganin sojojin Amurka sun fi karkata wajen goyon bayan jam'iyyar Republican.
Mista Swenson ya ce, ''Ba zan yi mamaki ba idan jam'iyyar Democrat ta samu ƙuri'u masu yawa na waje. To amma duk da haka akwai masu zaɓen da yawa da suka tuntuɓe mu a kan wanan zaɓen ciki har da waɗanda za su yi zaɓen a karon farko.''
Wani daga cikin irin waɗannan da ya tattauna da BBC, Chris, wanda aka ɓoye sunansa na ainahi wanda yake aiki a Birtaniya, wanda doka ba ta ba shi dama ya bayyan ra'ayinsa na siyasa ba, wanya ya fito daga jihar New Jersey amma kuma bai yi rijistar zaɓe ba duk da kasancewarsa mai goyon bayan Trump.
Amma a wannan shekarar ya yi rijista ganin yadda zaɓen zai kasance kankankan.
Ya ce, ''kasata na fama da hauhawar farashin kaya da kuma matsalar yawan baƙi, ba na jin Trump ƙwararre ne, amma dai ya fi Harris, dacewa wajen magance waɗannan matsaloli.
Ba wani ɗan takarar shugaban ƙasa na Republican da ya yi nasara a New Jersey tun 1988, amma Chris na ganin sauran masu zaɓe na Republican ma a jihohin da ba su da tabbas na da irin ra'ayinsa.
Ya ce, '' A 2016 babu ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da ta bai wa Trump nasara kuma ya yi nasara. Mutane da dama a can magoya bayan Trump ne amma ba sa magana.''

Asalin hoton, Getty Images











