Fari a Somalia: Yadda dokokin Amurka ke hana agaji isa ga masu bukatarsa

An wallafa

Kimanin mutum miliyan takwas na fuskantar matsananciyar yunwa a Somaliya kuma fiye da mutum 213,000 na iya halaka bayan da aka shafe shekaru uku ba a yi ruwan sama a kasar ba, kamar yadda wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya sanar.

Saboda haka abu ne mai faranta rai a ce tallafin dala biliyan 1.46 da Majalisar ta shirya tura wa kasar ya kai kimanin kashi 70 cikin 100 na abin da aka shirya tarawa.

Sai dai har yanzu ba ta iya raba abinci da ruwa da kuma kudade ga wadanda suka fi bukatarsu ba.

Wani babban jami'i da baya son a ambaci sunansa ya ce dokokin yaki da ta'addanci na Amurka ne ummul aba'isin aukuwar wannan matsalar.

Dokokin sun bukaci dukkan kungiyoyin da suka sami tallafi daga Amurka su tabbatar kayan agajin da suke rabawa bai shiga "hannun 'yan ta'adda ba" - kuma akasarin yankin kudancin Somaliya na karkashin ikon al-Shabab ne, kungiyar da ke da alaka da al-Qaeda kuma Amurka da Birtniya ke kallonta a matsayin kungiyar tadaddanci.

Wani jami'in wata kungiyar bayar da agaji ya koka: "Ba mu da ikon motsawa ko da na taki guda," kamar yada ya shaida wa BBC.

Kuma duk da cewa kungiyoyin na iya tura tallafi zuwa yankunan da gwamnatin kasar ke da iko, ba sa kai wa ga yankunan da al-Shabab ke da iko wuraren da akwai kimanin mutum 900,000 kamar yadda wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar.

Sannan wannan yankin ne ya fi fuskantar barazanar fari wanda ka iya zama gagarumar matsala.

Kungiyar bayar da agai da ta cimma burinta na tara kudaden tallafi ta ce a da tana dora alhakin gazawar raba agaji ne kan "karancin kudi", amma a yanzu babu wannan dalilin.

Al-Shabab na kai munanan hare-hare a Somaliya kuma ta kan zama karfen kafa ga yunkurin raba kayan agaji a kasar.

A misali, a shekarar 2011, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda kwamandojin al-Shabab ke karbar dubban dalolin Amurka kafin su kyale ma'aikatan kungiyoyin samun hanyoyin zuwa yankunan da ake bukatar agaji.

Al-Shabab ta rika hana wasu kungiyoyin shiga yankunan kuma ta rika kona magunguna da abinci har ma sun kashe wasu ma'aikatan agajin.

Sai dai duka da wannan yanayin, wani jami'i ya ce tilas su kulla yarjejeniya da al-Shabab - duk da barazanar Amurka na iya hukunta su - idan suna son kai agaji ga akasarin wadanda ke fuskantar fari da yunwa.

Me dokokin Amurka ke cewa?

Tattaunawa da al-Shabab bai taka dokokin Amurka ba - amma yin mu'amulla ta kudi wani abu ne na daban.

Akwai wasu jerin dokokin Amurka da suka haramta ba al-Shabab kudi.

Dukkan dokokin sun shafi ayyukan kungiyoyi masu raba kayan agaji, domin al-Shabab na karban kudaden haraji a wuraren da ta kafa shigayen bincike a kan hanyoyin shiga yankunan da suke iko da su.

Kungiyoyin raba kayan agaji sun ce biyan al-Shabab "haraji" laifi ne kuma dokokin Amurka sun hana su yin haka baki daya.

Sai dai dukkan wadannan dokokin biyu sun zama matsaloli sosai ga wasu kungiyoyin bayar da agaji, wadanda ke fargabar hukuncin da dokokin suka tanadar - na daurin shekara 20 a kurkuku da kuma tarar dala miliyan 1 ga dukkan wadanda aka kama da aikata laifi.

Kungiyar bayar da agaji ta gwamnatin Amurka USAid - wadda ke kan gaba wajen yawan agajn da ake raba wa a Somaliya - ta ce Amurkar ta ce tun 2011 ta ke aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya domin samar da hanyoyin kaucewa aikata laifukan da dokokin kasar suka hana aikatawa.

Wasu jami'an kungiyar sun bukaci a sassauta wani bangare na dokokin domin ba su damar cimma muradun kafa su.

"Sassautawa zai ba mu damar isa ga yankunan da ke bukatar taimako cikin lokaci," in ji wani jami'i.

Sai dai ba dukkan kungiyoin da Amurka ke da alaka da su ne suka ce takunkuman kasar na musu barazana ba.

Shugaban kungiyar Save the Children Binyam Gebru ya ce kungiyar USAid na duba yiwuwar taimaka wa kungiyarsa domin samun hanyoyin kai agaji zuwa yankunan da ke da wahalar shiga.

Franz Celestin, shi ne shugaban hukumar da kula da masu hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya, kuma ya yarda cewa jami'an gwamnatin Amurka na son ganin an kai agaji zuwa yankunan da ke karkashin ikon al-Shaba - amma suna so a kauce wa taka dokokin Amurkar.

Sai dai ya ce a karshe dole a tattauna tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da al-Shabab domin ba kungiyoyin agajin damar shiga yankunan da ke karkashin ikonta ba tare da sun biya "haraji" ba.

Mene ne tasirin al-Shabab ta amfana da kudin agaji?

Kowa ya san cewa al-Shabab ce kungiyar da ke iko da wasu yankunan Somaliya masu yawa in ji Nisar Maid, wanda malami ne a Jami'ar Tufts kuma mawallafin wani littafi da aka rubuta tare da wai marubucin kan farin da ya addabi Somaliya a 2011.

Ya ce "al-Shabab ta fi gwamnatin kasar iya tara haraji da kudaden shiga daga jama'ar da ke rayuwa a yankin nata da kuma kamfanonin da ke aiki a wuraren da ke karkashin ikonta."

Ya kuma ce dokokin kungiyar sun fi aiki idan aka kwatanta su da na gwamnatin Somaliya.

Wani rahoton da kungiyar Humanitarian Policy Group ta fitar a 2013 na cewa kudaden haraji da al-Shabab ke tarawa kalilan ne cikin tarin kudaden shiga da take samu.

Sai dai kudaden harajin na cikin dubban dalolin Amurka da suke samu a kowace shekara.

Farfesa Abdi Ismail Samatar masanin yanayin kasa a Jami'ar Minnesotta, kuma dan majalisar kasar Somaliya ne.

Ya ce sassauta dokokin Amurka da na Turai na iya sauya al'amura sosai ga 'yan Somaliya masu fuskantar matsananciyar yunwa da fari.

Kuma yayin da yankin ke fuskantar kamfan ruwan sama na shekara biyar a jere, da hauhawar farashin kayan abinci, bukatun al'ummar kasar za su karu.

Tilas a taimaka wa al'umomin yankunan da ke wannan kasar domin kauce wa matsalar halaka da ke jiran dubbansu.

Farfesa Samatar ya ce "tilas mu ceto su daga halaka kafin a ceto su daga hannun al-Shabab kuma yakar ta'addanci aiki ne mai dogon zango, amma ceto rayukan wadanda yaunwa ke daf da halakawa aiki ne na yanzu-yanzu."