Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kisan da aka yi wa wani babban jami'i na hukumar zabe zai shafi zabukan Kenya
Kawo yanzu yan Kenya ba su manta da zaben da aka yi a shekarar 2017 da ake zargin an yi magudi da kuma kisan gillar da aka yi wa wani babban jami’i mai kula da fasahar zabe, gabanin zabukan da za ayi a mako mai zuwa.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ya sha neman tabbatar wa jama’a masu shakkar cewa tawagarsa za ta iya bayar da sahihin kuri’u, amma kuma ya yi gargadin a kan wani wani shiri na musaman da aka kista domin batawa ma’aikatansa suna da kuma tsoratarsu musaman a kafofin sada zumunta.
Wafula Chebukati ya shaida wa manema labarai cewa, “Ma’aikatanmu musaman wadanda ke aiki a fanin kula da fasaha da harkkin intanet a yanzu sun firgita... Ina son na yi kira ga mutanen da ke wannan aiki da su daina abin da suke yi”.
Yana da kwararan dalilai shi yasa ya ke nuna damuwa saboda a shekaru biyar da suka gabata na yi awon gaba da tare da kashe shugaban fasahar hukumar Chris Msando tare da wata abokiyar huldarsa Carol Ngumbu mai shekara 21.
Na gano gawarwakinsu a cikin dazuka da ke wajan garin Nairobi kuma babu wani da aka kama ko ake tuhuma game da kashe kashen.
"Tabbas tare da kwararrun ‘yan sanda da kuma gwamnati mai inganci dan mun shawo kan wannan batu."
"Al’ummar kasar ba su san wanda ya kashe jami’in hukumar zaben ba wanda ya ke kula da wani muhimin sashe na zaben,” kamar yadda babban daraktan kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International Irungu Houghton ya shaidawa wani gidan talibijin na cikin gida.
Cikin kwanciyar hankali da natsuwa, Mista Msando ya kasance mai yawan aiki a gidajen Talibijin na cikin gida, inda ya nuna irin matakan da ya dauka domin tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe.
"Ba za a yi aringizon kuriu a karkashina ba," in ji shi a wata hira
Ya ba da kwarin gwiar sa ga naurar da ke dauke bayanan masu kada kuri'a da ke tantance masu kada kuria ta hanyar daukar hoton yatsu da kuma naurar watsa sakamakon zabe.
An fara amfani da irin wannan fasahar ne sakamakon abinda ya faru a zaben 2007, lokacin da aka yi zargin cewa an yi magudin zabe abinda kuma ya haifar da barkewar tarzoma na tsawon makoni inda mutum akalla 1,200 suka rasa rayukansu ya yin da 600,000 suka tsere daga gidajensu.
A wancan lokaci shugaban hukumar zabe na wancan lokaci ya amince da cewa bai tabbatar da wanda ya ci zaben ba.
Alamu sun nuna cewa za a yi fafatawa mai zafi a wannan zabe na shugaban kasa tsakanin yan takarar da ke gaba-gaba Raila Odinga, wanda ya dade yana jagorancin jam’iyyar hammaya da ke neman shugabancin kasar karo na biyar da kuma mataimakin shugaban kasa William Ruto.
Fasaha ba ita ce Dimokuraddiya ba
Abin da ya kara daukar hankali shi neshi ne yadda shugaban kasa mai baring ado Uhuru Kenyatta ya ke goyon bayan Mista Odinga wanda a baya babban abokin hammayarsa ne amma yanzu ya koma abokinsa kuma shi ne yake son ya gaje shi bayan da dangantakarsa da Mista Ruto ta yi tsami.
Masu kada zabe za su zabi gwamanoni da sanatocci da ‘yan majalisar wakila da kuma na kananan hukumomi.
Sai dai duk karuwar amfani da fasaha a zabuka uku da aka yi tun bayan 207 ba bu wani abin a zo a gani wajan samar da sahihin zabe kuma a shekarar 2017 sai da kotun koli ta soke zaben kuma ta bada umurnin sake gudanar da sabon zabe.
"Duk da matsalolin da suka kunno kai a 2013 an karo karin kayan fasaha a zaben 2017.
"Kudin da ke kashewa kan kowane mai kada kuria ya tashi daga dala 10 a zaben farko zuwa dala 25 a zaben da aka sake gudanarwa, abin da ya sa aka yi wa Kenya lakabi da kasar da ta fi kashe kudi wajan gudanar da zabe a Afrika”, in ji Nanjira Sambuli mai sharhi kan fasaha da shugabanci.
"Fasaha ba Dimokradiyya ba ce" in ji Ms SambuliKotun koli ta yanke hukunci a watan Ogustan 2017 cewa zaben ba shi da sahihanci ya yin da wasu rumfuna zabe 10,000 sun gaza tura da kuriun da suka tattara.
"Wannan adadi mai yawa, kuma hukumar zabeta bayar da uzuri lokacinda aka bukacesu ta bude na’urorin kwamfuta don duba abinda ya faru," Kamar yadda James Mambleo masanin kundin tsarin mulki ya shaidawa BBC.
Hukuncin kotun ya nunu ba bu kwarin gwiwa kan Mr Chebukati amma duk da haka ya ci gaba da rike mukaminsa duk da cewa ya rika fuskantar matsin lamba domin ya sauka daga mukaminsa.
A wannan karon hukumar za ta sake amfani da dubban naurorin tantance masu zabe da aka saya a lokacin zaben 2017 kuma ta inganta kaidojinta.
Masu zabe da aka tantance da naurar daukar hoto da na yatsu ne kawai zasu kada kuri’a kuma ta intanet ne zaa tura da sakamakon daga rumfunan zabe fiye da 50,000 a maimakon sakon waya wanda a baya shi ne tsarin da aka yi amfani da shi.
Yadda za a gudanar da zaben shugaban kasa:.
- Dole ne a tabbatar da duk masa kada kuri’a ta amfani da hoton yatsu da katin shaidar zama dan kasa.
- Bayan an rufe rumfunan zabe za a tura hoton fom din dauke da sa hannun jami’in hukumar zabe da wakilan jam’iyyu zuwa cibiyar tattara sakamakon zabe ta hanyar amfani da intanet .
- Za a ba dukkanin wakilan jam’iyyun siyasa kwafi kwafi na fam din kuma za a wallafa a wajan rumfunan zabe.
- An tsara naurorin zaben ta yadda za su iya aiki ne kawai a rumfunan zabe domin hana magudi
- Za a bayanna wanda ya ci zaben ne kawai idan idan hukumar zabe ta tantance sakamakon kuri,un da aka kirga da kuma hoton sakamakon zabe da aka turo ta intanet.
"Za mu kokarin ganin cewa ba mu ba mutane damar zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben da ba a sanar ba, saboda mun yi adalci da gaskiya a zaben kuma ko da sun je kotu za su ji kunya” a cewar daya daga cikin kwamishinonin hukumar zaben kasar, Justus Nyangaya.
Ya kuma ce naurar tantance masu kada kuri’a za ta rika aikewa da bayanai zuwa cibiyar tantance masu kada kuri’a a duk bayan sa’abiyu domin dakile yunkurin aringizon kuri'u.
Yayin da kawo yanzu ba a manta da abin da ya faru a zaben baya ba shugaban hukumar zaben Kenya ya yi kira ga kafofin watsa labarai da jam’iyyu siyasa da kungiyoyin farar hula da su ma su kirga kuri’un.
"Chebukati yana da anniyar yin gyara ta hanyar daukar alhakin duk wani abun da ya faru a matsayinsa na shugaba tare da aiwatar da wani tsari da zai tabbatar da an yi sahihin zabe.
"Ya yi hakan ne don ya wanke kansa daga abubuwan da suka faru a lokacin mutumin da ya gaji shugabancin hukumar zabe daga hannunsa wanda ake zargi da magudin zabe," in ji Hesbon Owila mai sharhi a kan harkokin siyasa.
"A matsayinsa na mutum ya koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya amma a matsayinmu na ‘yan kasa ya kamata mu yi taka tsan-tsan."
Mr Mamboleo ya amince da cewa: "Shin ko hukumar zabe ya yi kokarin yin aiki da kaidojin da kotun koli ta gindaya mata a hukunci da ta yanke a shekarar 2017?
"A ra’ayina eh. Sun rika tuntubar ‘yan siyasa da jama’a ta hanyoyin da bamu taba gani ba a zabukan baya.”
Kiraye kirayen da ake yi domin tabbatar da adalci
Bisa doka, hukumar zabenKenya tana da kwanaki bakwai bayan kada kuri’a ta bayyana wadanda suka yi nasara kuma ta hanyar karfafa wa kafofin yada labarai da sauransu gwiwa wajan kirga kuriu.
Mista Chebukati na fatan samu ingancin zabe zai wanke shi da hukumar.
Tabbas wannan zai zama muhimin ci gaba ga Kenya idan har aka cimma hakan.
Yayin da iyalan Mista Msando da Ms Ngumbi suka yi aduo'i cikarsu shekara biyar da mutuwa a watan daya gabata.
Sun ce ya kamata a dora dimokuradiyyar Kenya kan doka da oda kuma suna fatan wata rana su ma za a yi mu su adalci.
"Addu'armu ita ce wata rana mu san gaskiya”,iyalin Mista Msando sun rubuta haka a cikin wata jarida a ranar zagowar mutuwarsa