Arsenal za ta yi wasa tara a cikin watan Oktoba

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 1 ga watan Oktoba za a ci gaba da wasannin Premier League, karawar mako na takwas da za a yi fafatawa bakwai a ranar.
Arsenal tana ci gaba da jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City mai maki iri daya da na Tootenham ta uku.
To sai dai Arsenal za ta buga wasa tara a cikin watan na Oktoba ciki har da fafatawa hudu a gasar Euuropa League.
Gunners din za ta kece raini a wasa biyar a Premier League, bayan da ake sa ran dage wanda ya kamata ta yi da Manchester City ranar 19 ga watan Oktoba.
Arsenal za ta karbi bakuncin PSV Eindhoven ranar 20 ga watan Oktoba, hakan ne zai sa a dage fafatawar hamayya da ya kamata ta yi da kungiyar Etihad.
Wasannin mako na takwas ranar Asabar 1 ga watan Oktoba
- Arsenal da Tottenham Hotspur
- FC Fulham da Newcastle United
- Liverpool da Brighton & Hove Albion
- Southampton da Everton
- Crystal Palace da Chelsea
- AFC Bournemouth da Brentford
- West Ham United da Wolverhampton
Wasannin mako na takwas ranar Lahadi 2 ga watan OOktoba
- Manchester City da Manchester United
- Leeds United da Aston Villa
- Leicester City da Nottingham Forest
Wasannin da Arsenal za ta buga a cikin watan Oktoba
Premier League Asabar 1 ga watan Oktoba
Arsenal da Tottenham
Europa League Alhamis 6 ga watan Oktoba
Arsenal da Bodo Glimt
Premier League Lahadi 9 ga watan Oktoba
Arsenal da Liverpool
Europa League Alhamis 13 ga watan Oktoba
Bodo Glimt da Arsenal
Premier League Lahadi 16 ga watan Oktoba
Leeds da Arsenal
Premier League Laraba 19 ga watan Oktoba
Arsenal da Man City
Europa League Alhamis 20 ga watan Oktoba
Arsenal da PSV Eindhoven
Premier League Lahadi 23 ga watan Oktoba
Southampton da Arsenal
Europa League Alhamis 27 ga watan Oktoba
PSV Eindhoven da Arsenal
Premier League Asabar 30 ga watan Oktoba
Arsenal da Nottm Forest











