Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Man United

Arsenal vs Man United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta za ta karbi bakuncin Manchester United ranar Lahadi a gasar Premier League a Emirates.

Arsenal tana matakin farko a kan teburi da maki 47, ita kuwa United tana ta hudu da makinta 39.

Wannan shi ne wasa na biyu da za su fafata a kakar nan, bayan karawar ranar 4 ga watan Satumbar 2022, inda United ta yi nasara da ci 3-1 a Old Trafford.

Wadanda suka ci wa United kwallayen sun hada da Anthony Martial da Marcus Rashford, wanda ya zura biyu a raga, Bukayo Saka ya ci wa Arsenal dayar.

Arsenal za ta yi fafatawar ta hamayya ba tare da Gabriel Jesus da Reiss Nelson, wadanda ke jinya.

Gurners na jiran jin sakamakon ko sabon dan kwallon da ta dauka Leandro Trossard ta kammala yi masa rijista ko zai iya buga karawar ta Lahadi.

United za ta buga wasan ba tare da Casemiro ba, wanda ke hukuncin dakatarwa wasa daya, bayan da ya karbi katin gargadi biyar.

Jack Butland na kan ganiya, bayan da bai fuskanci kungiyarsa ta Crystal Palace ranar Laraba da suka tashi 1-1 a kwantan Premier League.

Abin da ya kamata ku sani a haduwa tsakanin kungiyoyin

Arsenal ta ci United a wasa biyar daga bakwai a bayan nan da ta karbi bakuncin kungiyar Old Trafford da yin canjaras daya da rashin nasara a daya.

Wasa 11 daga 17 da Arsenal ta yi nasara a irin karawar nan a ranar Lahadi ta buga.

United ta kasa cin wasa a karawa shida a tara baya a lik da ta ziyarci Gunners.

Arsenal vs Man United

Asalin hoton, BBC Sport

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Arsenal

Wannan shi ne karo na uku da Arsenal za ta karbi bakuncin United tana matakin farko a teburin Premier, sauran biyun canjaras suka yi 1-1 a 2004 da kuma 2-2 a 2007

Arsenal ta ci wasa hudu daga biyar da ta yi da 'yan biyar din farko a bana a Premier, United ce ta doke 3-1 a Satumba kadai.

Sai dai Gunners ba ta ci wasa biyar a kan 'yan biyar din farko a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ba tun kakar 2007/08.

Gunners ta ci kwallo a wasa 17 daga 18 da ta fafata, in banda wanda ta tashi 0-0 da Newcastle United.

Bukayo Saka na fatan cin United a karawa uku a jere a Premier League - 'yan wasan Arsenal da suka yi wannan kwazon sune - Freddie Ljungberg da kuma Thierry Henry.

Gabriel Martinelli yana da hannu da Arsenal ta ci kwallo 10 a Premier League a Emirates, wanda ya ci shida ya bayar da hudu aka zura a raga.

Manchester United

Wasan da Manchester United ta yi 1-1 da Crystal Palace ya kawo karshe cin karawa tara da ta yi a jere da kuma fafatawa 15 da take lashe wasa idan ita ta fara cin kwallo a raga.

United na fuskantar barar da maki a wasa biyu a jere a karon farko a Premier League, tun bayan wanda ta yi a tsakaninta da Brighton da Brentford a wasa biyu da fara kakar bana.

Watakila United ta ci wasa na shida a waje a bana, irin bajinatr da ta yi a bara kenan, kuma biyar da ta yi nasara a kakar nan kowanne 1-0 ta ci.

Marcus Rashford ya ci Gunners kwallo hudu ya kuma bayar da hudu aka zura a raga a wasa 10 da ta fuskanci Arsenal, kungiyar da yafe ci kenan.

Sai dai Rashford ya kasa zura kwallo a raga a wasa 26 da ya yi a karawar waje kusan shekara biyu kenan a Premier League.