Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Garuruwa biyu a Najeriya da ake ƙauna da ƙyamar tagwaye
A lokacin da tawagarmu ta isa wani dan karamin gari - da ake yi wa lakabi da 'garin tagwaye', domin yin bincike kan yawaitar haihuwar tagwaye da ake yi a kauyen da ake kira Igbo-Ora - muka yi kicibis da labarin haihuwar wasu tagwayen a wani karamin asibiti da ke garin.
Mahaifiyar yaran - wadda ita ma 'yan biyu aka haifeta, mu samu dan biyun nata a dakin asibitin yana daukar sabbin tagwayen hoto.
A gefen gadon da tagwayen ke kwance kuwa kakarsu ce a zaune - wadda ita ma 'yan biyu ce, sannan kuma ga kakar mahaifiyarsu, wadda ta haifi tagwaye har sau biyu.
"Mu a nan garin haka abin ke faruwa. Mukan haifi tagwaye. Hakan ya sa garinmu ya zama na musamman," kamar yadda kakar sabbin jariran ta shaida wa BBC.
"Muna alfahari da hakan kuma muna kaunarsu, muna son tagwayenmu, sun kawo mana nasaroti masu yawa," in ji ta.
"Munate ba sa jin dadin idan ba su haifi tagwaye ba."
Magana ta gaskiya garin Igbo-Ora, da ke kudu maso yammacin Najeriya ya fi kowane gari yawan tagwaye, idan kana tafiya a cikin garin abu ne mai sauki ka iya jerin tagwaye masu yawa , wadanda galibi ke sanye da tufafi iri daya.
Matsakaicin samun haihuwar tagwaye a duniya shi ne 12 a duk haihuwa 1,000, amma a garin Igbo-Ora an ce a cikin kowacce haihuwa 1,000 akan samu tagwaye 45.
A al'adun Yarabawa, wadanda suka mamaye kudu maso yammacin kasar, haihuwar tagwaye wata albarka ce, kuma suna da sunayen da al'ada ta tanadar musu.
Idan tagwayen sun fara girma akan kira su da suna 'Taiwo' ko da mata ne ko kuwa maza.
Taiwo na nufin 'wanda ya dandani rayuwar duniya', yayin da ake kiran kananan 'Kehinde' wanda ke nufin 'wanda ya zo daga baya''.
Washegari muka ziyarci makarantar sakandiren garin, inda muka tarar cewa wadannan sunaye sun mamaye makarantar, ko'ina kiran sunayen ake yi.
A lokacin da daliban suka taru a wurin asambule su kusan 1,500, mun tambaye su cewa duk wanda ya san shi tagwai ne ko kuma akwai tagwaye a gidansu su daga hannu,kusan kowa a cikin ya daga hannunsa sama.
Me ya sa ake samun yawaitar tagwaye a garin?
A labaran kunne ya girmi kaka, yariman masarautar Oyo ne ya kafa kauyen a karni na 14, lokacin da aka fitar da shi daga masarautar, inda aka bukace shi ya ya yi wa ta sadaukarwa ta musamman ga ababen bautar Yarabawa, lamarin da ake ganin ya sa kauyen ya samu albarkar tagwaye.
Da yawa daga mazauna kauyen na tunanin cewa suna cin kwayoyin halittar da ke sa su samu tagwayen ne a a bincin da suke kira ''ilasa'', da ake yi daga ganyen okra.
Ana zuba ganyen a cikin tukunya inda ake tafasa shi tare da gishiri da sauran kayayyakin kamshi, da irin kankana da 'ya'yan dorawa.
Dalilin da ya sa ake yawan haifar tagwaye a garin Igbo-Ora abu ne da ke bukatar zurfafa bincike.
Kadan ne daga cikin tagwayen da ake haihuwa a kauyen ke kama da juna - wadanda binciken masana ya ce suna samuwa ne daga kwan halittar namiji guda da ya rabu biyu bayan shigarsa mahaifa.
Mafi yawan tagwayen kauyen ba sa kama da juna, abin da ke nufin kwayayen halittar daban-daban ne suka shiga mahaifar mace a lokaci guda.
Masana na bincike kan ko samun tagwayen da ake yi a na da ala da abincin da mazauna kauyen ke ciki, irin su ilasa ko kuma doyar da ake nomawa a kauyen, ne ke sa matan ke samanr da kwayaye masu yawa.
Farfesa Akintola Kehinde Akinlabi, shugaban makarantar kwalejin aikin gona da fasaha ta jihar Oyo, wadda ke kauyen, na ganin cewa kwayoyin halittun gado ne ke sanya hakan.
Masanain - wanda shi kansa 'yan biyu aka haife shi, ya kuma haifi tagwaye - ya ce wanda aka haifa a matsayin tagwai a kauyen ba zai yi wahalar samun miji ko mata ba.
"Ana daukar tagwaye a masayin wata ni'ima daga ubangiji da za ku zako kyakkywar makoma da kariya ga dangi. Mutane kan bai wa tagwaye kyaututtuka na kudi domin neman taimakonsu. Duka wadannan abubuwan kan sa mutane su auri tagwaye, tare da fatan samun haihuwar tagwayen,'' in ji shi.
Mai garin kauyen da ake kira oba, na cike da zumudin jiran sakamakon binciken da aka yi game da haihuwar tagwaye a garin.
Dagacin, mai suna Jimoh Olajide na fatan cewa yadda 'yan NAjeriya ke fatan shiga kundin adana kayan tarihi na Guinness, za su taimaka garin ya shiga cikin wannan kundi, saboda baiwar da Allah ya yi wa garin na haihuwar tagwaye, inda kusan kowane gida a kauyen aka haifi akalla tagwaye sau daya.#
"Burina shi ne kauyenmu ya shiga cikin kundin adana abubuwan tarihi na Guinness na zama garin da ya fi kowane gari haihuwar tagwaye a duniya,'' in ji Oba Olajide, wanda shi ma uba ne ga tagwaye.
"Daga nan kuma a sanya garin cikin wuraren yawon bude ido, inda za a gina manya-manyan otal-otal."
Kan wanna kuduri ne garin ya bullo da bikin tagwaye na shekara-shekara da aka shafe shekaru ana gudanarwa.
Farfesa Akinlabi na fatan mayar da hankali kan tagwayen, zai a sa a samu zuba jari da zai magance matsalolin da kauyen ke fuskanta kamar rashin kyawun yanayin asibitocin kauyen.
Duk duk da addinin Musulunci da na Kiristanci da ake yi a yankin, ba a ajiye al'adar yi wa tagwayen wani nau'in ibada ba.
Kehinde Adeleke, daya daga cikin matasan kauyen - wadda ita ma 'yan biyu ne ta kai mu wurin da ake yin wannan tsafi, inda ake shan giyar wake, a la'dar yankin abin bautarsu ya yarda danginsu, shi ya sa ake ba su tagwaye.
"Ina jin dadi kasancewata wadda aka haifa 'yan biyu," in ji Ms Adeleke wadda ta haifi 'ya'yan biyu, sai dai har yanzu ba ta haifi tagwaye ba tukunna.
"Zan ji ba dadi idan ban haifi 'yan biyu ba, domin kuwa ina bukatarsu,'' in ji ta a lokacin da take waka a wurin bikin tagwaye na shekara-shekara da ake gudanarwa.
Wannan dabi'a ta son tagwaye, ta saba wa al'adun kauyen Bassa-Komo da ke kusa da Abuja, babban birnin kasar, wadanda suke daukar tagwaye a mtsayin abin kyama.
A tsakiyar shekarun 1990, wani dan mishan mai suna Olusola Steven ya ji daga bakunan 'yan kauyen cewa tagwaye abin kyama ne, kamar wata tsinuwa ce ga dangin da suka haife su.
Wannan wata mummunar dabi'a ce da ta samu karbuwa musamman a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda wasu al'ummun suka rika kashe tagwaye a baya, kodayake tuni aka dakatar da wannan dabi'a da dadewa.
Fasto Steven, da ke zaune a unguwar Gwagwalada, kimanin kilomita 600 daga arewa maso gabashin kauyen Igbo-Ora, ya yanke shawarar gudanar da bincike.
"Mun fara zuwa gari-gari muna tambayarsu cewa ina tagwayen?, amma duka amsa guda muke samu cewa ubangiji ya kashe su. A wasu lokutan ma mahaifiyarsu ko shayar da su ba ta yi, don haka yunwa ke kashe su,'' in ji shi.
Malaman mishan din sun gano cewa a wasu lokutan akan bai wa jariran tagwayen wani ganye da za su ci wanda zai hana su girma.
Ba a san dalilin da ya sa al'ummar kauyen ke kallon tagwayen a matsayin wani abin kyama ba, amma watakila hakan ba ya rasa nasaba da yadda aka rika camfin cewa haihuwar tagwaye na janyo hatsarin yawan mace-mace a cikin al'umma.
Fasto Steven da tawagarsa sun fara kubutar da tagwayen inda suka gina gidan kula da marayu da suka sanya wa suna ''The Vine Heritage'', wanda a yanzu ke kula da yara kusan 200.
Domin sauya wa mutanen kauyen tunani, sun fara kai wa kauyen tallafin magunguna, da samar musu da tsaftatccen ruwan sha.
Gidan marayun da suka kafa na aiki da kungiyar agaji ta Actin Aid domin daukar nauyin shirye-shirye tare da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai. A nata bangare ita ma gwamnatin Najeriya ta rika daukar nauyin gangamin wayar da kan jama'ar yankin dangane da tagwayen
Da hakan ne al'ummar kauyen Bassa-Komo suka rika ganewa tare da barin tagwayen da suka haifa su rayu da su, amma da iyayen da hankalinsu bai kwanta da tagwayen ba, sukan bayar da su ga gidan marayun, inda suke zuwa lokaci-lokaci domin ziyartar su.
A takaice dai kimanin yara 27 ne suka amince da bukatar iyayensu na komawa gida, domin ci gaba da rayuwa da iyayen nasu, duk da cewa matakin ba mai sauki ba ne ga yaran.
"Lokaci na farko da na fara ganin mahaifina shi ne lokacin da na kai shekara 18, na ji takaicin yadda ya yi watsi da ni,'' in ji Olufemi Stevens, da ake yi wa lakabi da ''Wonder Boy".
Ya girma a gidan marayu bayan da mahaifiyarsa ta rasu a lokacin haihuwa, amma a yanzu ya yi sa'ar komawa gidan yalansa. ''A lokacin da suka ganni sun fahimci cewa ashe mu ba abin kyama ba ne''.
"A lokacin da na koma gida, na yi mamaki yadda na ga wasu tagwayen tare da iyayensu. Fatana shi ne kafa makaranta ta musamman a kauyenmu, domin ilimi shi ne muhimmin abu,''
Fasto Stevens ya ce mutanen kauyen Bisso-Koma ba za su taba son tagwaye kamar yadda ake kaunar su a kauyen Igbo-Ora, amma yana fatan cewa wata rana mutanen kauyen za su fahimci ayyukansa.