'Mai yiwuwa China ta aikata laifukan cin zarafi kan Musulman Uyghur'

An wallafa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi China da aikata “manyan take hakkokin ɗan adam” a wani rahoto da aka daɗe ana jira na zargin cin zarafi a yankin Xinjiang.

China ta buƙaci MDD da kar ta saki rahoton tana mai karyata bayanan, wadanda ta ce an hada baki ne da kasashen Yamma don a yaga mata rigar mutunci a idon duniya.

Rahoton ya bayyana zarge-zargen cin zarafin Musulman Uyghur da sauran ƙabilu marasa rinjaye, lamarin da China ta yi watsi da shi.

Amma masu bincike sun ce sun gano “ ƙwararan hujjoji” na zabtarwa da laifukan take hakkin ɗan adam.

An saki rahoton ne a ranar ƙarshe ta aikin babbar jami’ar MDD kan hukumar hakkin ɗan adam Michelle Bachelet.

A tsawon lokacin da ta ɗauka tana aiki, an yi ta gabatar da zarge-zarge na cin zarafin Musulman Uyghur.

Rahoton tawagarta ya zargi China da amfani da dokokin tsaron ƙasar marasa tsari wajen far wa da tauye dokokin tsirarun ƙabilu da kuma kame su da ake yi a kulle.

Ya ce ana azabtar da fursunonin da ma cin zarafi ta hanyar lalata da su.

Sannan ana yi wa wasu dole wajen ba su magunguna da tursasa musu yin tsarin iyali da ƙayyade haihuwa.

MDD ta ce dole China ta yi gaggawar ɗaukar matakan sakin “dukkan mutanen da aka hana su ƴancinsu na walwala” tare da cewa abubuwan da Chinar ta yi daidai suke da “manyan laifukan cin zarafi n aƙasa da ƙasa, da suka haɗa da na cin zarafin bil adama”.

A yayin da MDD ke cewa ba ta da tabbas kan yawan mutanen da gwamnatin ta tsare, ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun yi ƙiyasin cewa fiye da mutum miliyan ɗaya aka tsare a sansanoni a yankin Xinjiang, a arewa maso yammacin China.

Ƙungiyar Musulman Uyghur ta duniya ta yi maraba da rahoton tare da buƙatar ƙasashen duniya su ɗauki martani cikin gaggawa.

“Duk da dagewar da gwamnatin China ta yi na watsi da batun, a yanzu MDD ta fahimci cewa ana aikata miyagun laifuka,” a cewar hhugaban kula da kare hakkin Musulman Uyghur, Omer Kanat.

Akwai mutum miliyan 12 ƴan ƙabilar Uyghur waɗanda yawancinsu Musulmai ne da ke zaune a Xinjiang.

MDD a cikin rahoton ta ce lamarin na shafar har da su ma waɗanda ba Musulmai ba na ƙabilar.

Amurka da mahukunta a ƙasashe da dama a baya sun sha caccakar matakan China a Xinjiang, suna cewa hakan kisan kiyashi ne, amma MDD ta dakatar da irin waɗannan zarge-zargen.

Beijing – wacce ta ga rahoton kafin a sake shi – ta ƙaryata batun cin zarafi tana mai cewa an samar da sansanonin ne don a yi yaƙi da ta’addanci.

China ta sha nanata cewa mayaƙan sa kai na Uyghur na yaɗa aƙidar samun ƴancin ƙasarsu ne, amma an zarge ta da kambama girman barazanar don kawai ta nuna cewa zaluntar da take yi wa ƴan Uyghur ba laifi ba ne.

Tawagar ƙsar a taron hukumar kare hakkin dan adam ta MDD a Geneva a ranar Alhamis ta yi watsi da rahoton, wanda ta ce “an yi  ne don shafa mata kashin kaji da ɓata wa China suna” da kuma yin katsalandan a cikin harkokinta na cikin gida.

“Wannan rahoton ba komai ba ne illa tuggun siyasa da aka ƙi duban gaskiya da kuma tona asirin Amurka da ƙasashen yamma da maƙiyan China don amfani da hakkin dan adama a matsayin farfaganda,” a wata doguwar sanarwa da Chinar ta fitar.

Wane sauyi rahoton MDD zai kawo?

Sharhi daga Tessa Wong, Wakiliyar BBC a harkokin dijita na yankin Asia

A yanzu dai ya rage wa ƙasashen duniya su san abin yi. Tuni, masu faftukar kare hakkin dan adam na Uyghur suke kira da a samar da hukumar bincike, tare da neman masu ruwa da tsaki a ko ina a faɗin duniya da su yanke alaƙa da duk wani mai goyon bayan gwamnatin China kan abin da take yi wa ƴan Uyghur.

Batun ko ƙasashen duniya za su matsa lambar da za a samu wani sauyi abin yin muhawara akai ne.

Beijing dai tana ta nanata cewa duk wannan abin da ake yi ƙoƙari ne na ɓata mata suna, tana cewa babu wani zalunci da take aiwatarwa a wajen.

Ta ce a yanzu haka ma yankin Xinjiang ya samu ci gaba na walwalar jama’a da haɓakar tattalin arziki har ma ta kira hakan da “gagarumin ci gaban hakkin ɗan adam da aka samu.”

Rahoton MDD dai ya zama abin kunya, yana kawar da dagiyar China na cewa ita ɗin ƙasa ce mai mutunci a cikin ƙasashen duniya.

Amma binciken shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin rahotannin da aka sha fitarwa Beijing na yin watsi da su.

Sannan zai yi wahala a samu matsin lamba a cikin ƙasar ma.

Batun cin zarafin ƴan Uyghur bai taɓa zama abin nuna damuwa ga ƴan China ba, saboda abu ne da ya zama tamkar haramun a tattauna shi – ya zuwa ranar Alhamis da rana, babu wata kafar yaɗa labaran China da ta ambaci rahoton na MDD ko a shafukan sada zumunta.

Makomar ƴan Uyghur ta dogara ne kan lokacin da gwamnatin China za ta yanke shawarar kawar abin da take ganin a matsayin barzana ga ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a cikin al’umma.

A farkon shekarar ne BBC ta gano wasu bayanan sirri da suka nuna yadda ake tsara yi wa mata fyaɗe da cin zarafi da azabtar da Musulman Uyghur a sansanoni.

BBC ta ga bayanan rundunar ƴan sandan Xinjiang da suka nuna yadda ake fakon al’ummar bisa umarni tun daga wajen shugaban ƙsar China Xi Jinping.