Arsenal ta tuntubi Leeds United kan Raphinha

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta tuntubi Leeds United kan batun daukar dan wasa Raphinha.
An fahimci cewar wannan ne karon farko da aka tuntubi Leeds kan daukar dan kwallon Brazil din, wanda ya ci kwallo 11 a Premier League da aka karkare a bana.
Sai dai wasu rahotanni na cewar kudin da Arsenal ke son taya dan kwallon ya yi kasa da wanda Leeds za ta sayar da shi.
Mai shekara 25, ya koma Leeds United daga Rennes a 2020, wanda manyan kungiyoyi ke son zawarci har daga wajen Ingila.
Dan wasan na son buga tamaula a Barcelona, sai dai ba a tabbacin ko kungiyar Camp Nou na bukatar dan kwallon, sannan ko tana da kudin daukar dan wasan.
Raphinha ya ci kwallo 17 a wasa 60 a Premier League a Leeds United, wadda ake ganin watakila ta hana shi tafiya a bana.
Ana kuma cewar watakila Manchester City za ta bukaci yin musaya da Leeds United ta bayar da Raphinha ta karbi Kalvin Phillips.









