Chelsea ta tuntuɓi Nagelsmann da Enrique, Al-Hilal ta ɗauki hankalin Messi

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta tuntubi tsohon kociyan Bayern Munich Julian Nagelsmann, da kuma tsohon kociyan Sifaniya Luis Enrique, a zawarcin da take yi na sabon mai horarwa. (Telegraph)
Kungiyar a yanzu ba ta tunanin neman kociyan Brighton Roberto de Zerbi, domin maye gurbin Graham Potter. (Athletic )
Shi kuwa Potter dan Ingila mai yuwuwa ya zama kociyan West Ham nan gaba kasancewar kungiyar na duba yuwuwar rabuwa da David Moyes, da bazara. (Telegraph)
De Zerbi da Nagelsmann sun nuna cewa ba sa sha'awar karbar aikin horad da Tottenham. (90min)
Shi kuwa tsohon kociyan Crystal Palace, Patrick Vieira, zai iya kasancewa kociyan Nottingham Forest idan kungiyar ta yanke shawarar rabuwa da Steve Cooper. (Mail)
Mai yuwuwa Lionel Messi, ba zai cimma yarjejeniyar ci gaba da zama a Paris St-Germain ba. (ESPN)
Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta yi tayin bai wa Messi albashin sama da yuro miliyan 400 a duk shekara idan ya yarda ya koma can. (Fabrizio Romano)

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Liverpool da Tottenham sun nuna sha'awar sayen dan bayan Koriya ta Kudu Kim Min-jae da ke Napoli. (Mail)
Liverpool ta karkata ga sha'awar matashin dan wasan tsakiya na Brighton da Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21, bayan da Wolves ta bayar da damar sayen dan tsakiya na Portugal Matheus Nunes, abin da ya bude kofa ga Liverpool ta saye shi a kan fam miliyan 44 a bazaran nan. (Mirror)
Wolves na shirin zawarcin dan wasan tsakiya na Real Madrid da Sifaniya Dani Ceballos, saboda kwantiragin dan wasan mai shekara 26 zai kare a bazara. (90min)
Ajax na sha'awar sake sayen dan wasan tsakiya na Manchester United da Netherlands Donny van de Beek, a bazara. (Football Insider)
Watakila matashin dan gaban Serbia Dusan Vlahovic, ya koma Arsenal a bazara, bayan da ya yi ki Gunners din a watan Janairu ya zabi Juventus. (Four Four Two)
Liverpool za ta bar dan wasan tsakiya na Guinea Naby Keita, ya bar kungiyar kyauta a bazara. (Fabrizio Romano)
Sampdoria ba za ta rike dan wasan Tottenham da Ingila, Harry Winks, da ta karba aro ba, ya zama nata dindin saboda matsalar kudi da take fama da ita. (Sun)
Leicester da Aston Villa da Brentford da Brighton da kuma Crystal Palace na sha'awar dan wasan gaba na Feyenoord Santiago Gimenez, wanda kuma kungiyoyin Italiya da Faransa da Jamus suma ke bin diddigin dan Mexicon mai shekara 21. (90min)










