Alcantara ya yi ritaya bayan barin Liverpool

An wallafa

Thiago Alcantara ya yi ritaya daga taka leda, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a Liverpool.

Tsohon ɗan wasan tawagar Sifaniya, mai shekara 33 ya buga wasa ɗaya a kakar 2023-24 a ƙungiyar Anfield, sakamakon jinya.

Thiago wanda aka yi wa tiyata a ƙugu a 2022-23, bai warke ba sai cikin Fabrairun 2024, wanda ya koma wasa a karawa da Arsenal, inda ya kara jin ciwo a fafatawar.

Shi ne wasa na 98 da ya yi wa Liverpool tun bayan da ya koma ƙungiyar kan kaka hudu daga Bayern Munich a 2020.

Thiago ya lashe FA Cup a Liverpool a 2021–22, wanda a baya ya bayar da gudunmuwar da Bayern ta ɗauki Bundesliga a kaka bakwai da Champions League a 2019–20.

Ya fara tamaula a Barcelona da ɗaukar La Liga da Champions League ɗaya daga nan ya koma Bayern a 2013.

Wanda aka haifa a Italiya - mahaifinsa tsohon ɗan wasan tawagar Brazil, Mazinho ne a lokacin da yake murza leda a Lecce.

Thiago ya koma Barca a lokacin da yake da shekara 14 ta haihuwa, ya wakilci Sifaniya, wadda ya buga wa karawa 46 tsakanin 2011 zuwa 2021.