Sir Jim Ratcliffe na daf da sayen hannun jari a Man United

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran za a amince da yarjejeniyar Sir Jim Ratcliffe ta zama mai ƙaramin hannun jari a Manchester United a lokacin hutun wasannin ƙasa da ƙasa na watan Nuwamba, watakila a farkon mako mai zuwa.
Ana tsammanin rukunin kamfanonin Ineos na Ratcliffe zai biya kusan £1.25bn don sayen kashi 25 na hannun jari.
Iyalan Glazer na United sun sanar a ranar 22 ga watan Nuwamba 2022 cewa suna tunanin siyar da kulob ɗin.
Ineos da ɗan ƙasar Qatar Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani sun taya kulob ɗin, inda suka gabatar da tayin kusan £5bn.
Sheikh Jassim ya janye daga tsarin ne a watan da ya gabata, yana mai iƙirarin cewa tayinsa na ƙarshe, wanda ake tunanin ya ninƙa darajar dalar Amurka biliyan 3.2, sai dai bai gamsar da Glazers ba.
Ratcliffe ya sauya niyyarsa ta farko na siyan hannun jarin kashi 69 mallakan Glazers kuma ya rage shi zuwa "mafi rinjaye".
Amma sai lokacin da ya sake rage shi, zuwa kashi 25 shi ne tsammanin, yiwuwar ƙulla yarjejeniyar ta karu.
Ratcliffe, wanda ya ce shi masoyin United ne na tsawon rayuwarsa, ya yi koƙarin siyan Chelsea a bara.












