Ina da yaƙinin 'yan wasanmu za su farfaɗo da United - Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce ya yi amanna da hazaƙar 'yan wasan ƙungiyar kuma sun ƙuduri aniyar inganta yanayin da ƙungiyar ke ciki a halin yanzu.
An yi waje da United daga gasar cin kofin Carabao a tsakiyar mako inda Newcastle United ta bi ta har gida ta doke ta da ci 3-0.
Rashin nasarar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ke tangal-tangal a farkon kakar wasan gasar Premier, inda kulob ɗin na Old Trafford ke matsayi na takwas da maki 15 bayan wasanni 10.
"Suna so su inganta wannan lamarin," in ji Ten Hag game da tawagarsa.
Ya ƙara da cewa "za mu yunƙuro, 'yan wasanmu na da ƙarfi, masu horaswan na da ƙwazo kuma kocin yana da hikima."
United ta sha kaye a hannun abokayar hamayyarta Manchester City da ci 3-0 kafin ta yi rashin nasara a wasan Newcastle.
A ranar Asabar ne kuma za ta ziyarci Fulham a gasar Premier League.








