Ko Liverpool za ta ci Newcastle United kuwa?

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool za ta karbi bakuncin Newcastle United a wasan mako na biyar a gasar Premier League da za su fafata ranar Laraba a Anfield.
Liverpool tana ta 12 a teburi da maki biyar, ita kuwa Newcastle mai maki shida tana ta 10 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
A kakar bara Liverpool ta yi nasara gida da waje, inda ranar 16 ga watan Disambar 2021 ta yi nasara da ci 3-1 a Anfield.
A wasa na biyu a St James Park kuwa ranar 30 ga watan Afirilun 2022, Liverpool ta ci 1-0.
A wasa 26 da Liverpool ta buga a gida a Premier League da Newcastle United, Liverpool ta ci wasa 21 da canjaras biyar, tun bayan cin 2-0 da Newcastle ta yi a Anfield a Afirilun 1994.
Newcastle ta doke Liverpool 2-0 a St James Park a Disambar 2015 daga nan ba ta yi nasara a kan Liverpool ba a karawa 11 a Lik da canjaras hudu da shan kashi a wasa bakwai.
Liverpool ta yi wasa 25 a gida a jere a Premier League ba tare da an doke ta ba, wadda ta ci 19 da canjaras shida a Anfield tun bayan 1-0 da Fulham ta yi mata ranar 7 ga watan Maris din 2021.
Liverpool ta yi nasara a wasa 10 daga 11 da ta buga a baya a tsakiyar mako da yin nasara a karawa shida baya da cin kwallo 18-2.
Ita kuwa Newcastle ta ci wasa biyu kwanan nan da ta kara ranar Laraba, wadda ta yi nasara a fafatawa daya daga 24 a can baya da canjaras biyar da shan kashi a wasa 18.
A kakar bara a Premier League Newcastle ta yi rashin nasara a wasa shida da kungiyoyin shidan farko a teburi da cin kwallo shida aka zura mata 20 a raga.
Eddie Howe ya yi rashin nasara a wasa takwas a jere a hannun Liverpool tun bayan 2-2 da suka tashi a Anfield A Afirilun 2017 a lokacin yana Bournemouth.
Liverpool da Newcastle United kowacce ta saka 'yan wasa bakwai masu shekara 30 ko fiye da haka a Premier League ta kakar nan.
Roberto Firmino yana da hannu a kwallo biyar daga 9-0 da Liverpool ta doke Bournemouth ranar Asabar.
Liverpool ta ci Newcastle United kwallo 109 a gasar Premier, kungiyar da ta zazzagawa kwallaye mafi yawa a wasannin.











