Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasanni masu zafi da Liverpool za ta yi a watan Oktoba
Ranar 1 ga watan Oktoba Liverpool za ta ci gaba da buga wasan Premier League, kuma daya daga wasa tara da za ta yi a cikin watan Oktoba.
Liverpool za ta fara da karbar bakuncin Brighton a Anfield, daga cikin fafatawa shida da za ta buga a babbar gasar tamaula ta Ingila a watan na 10.
Haka kuma Liverpool za ta yi wasa uku a Champions League da ya hada da karbar bakuncin Rangers, sannan ta ziyarci Scotland a wasa na biyu a gasar Zakarun Turai.
Haka kuma Liverpool za ta ziyarci Ajax a wasa karo na biyu a Champions League, bayan da ta yi nasara da ci 2-1 a Anfield a kan kungiyar Netherlands.
Liverpool mai maki tara tana ta takwas a kan teburin Premier da cin wasa biyu da canjaras uku da rashin nasara a gidan Manchester United a kakar bana.
Cikin wasannin da ake hangen Liverpool za ta fuskanci kalubale a wasan na Oktoba a Premier, sun hada da wanda za ta ziyarci Arsenal ranar 9 ga watan.
Ranar 16 ga watan na Oktoba Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester City a Anfield, ita kungiyar Etihad tana ta biyu da maki iri daya da na Totttenham.
Arsenal ce ke jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City da Tottenham.
Jerin wasannin da Liverpool za ta yi cikin Oktoba:
Premier League Asabar 1 ga watan Oktoba
- Liverpool da Brighton
Champions League Talata 4 ga watan Oktoba
- Liverpool da Rangers
Premier League Lahadi 9 ga watan Oktoba
- Arsenal da Liverpool
Champions League Laraba 12 ga watan Oktoba
- Rangers da Liverpool
Premier League Lahadi 16 ga watan Oktoban
- Liverpool da Man City
Premier League Laraba 19 ga watan Oktoba
- Liverpool da West Ham
Premier League Asabar 22 ga watan Oktoba
- Notting Ham Forest da Liverpool
Champions League Laraba 26 ga watan Oktoba
- Ajax da Liverpool
Premier League Asabar 29 ga watan Oktoba
- Liverpool da Leeds