West Ham ta kusan kammala cinikin Emerson Palmieri daga Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
West Ham ta kusan kammala cinikin mai tsaron baya, Emerson Palmieri daga Chelsea kan kudin da ake cewar zai kai fan miliyan 15.
Mai shekara 28 dan kasar Italiya ya buga wasannin aro a bara a Lyon, wanda ya kasa samun gurbin buga wasanni a Chelsea.
Dan kwallon ya koma Stamford Bridge da taka leda a 2018 daga Roma.
Za a kammala auna koshin lafiyar Emerson ranar Talata, sannan ya saka hannu kan kunshin yarjejeniyar da aka gabatar masa.
Dan kwallon da ya lashe Euro 2020 da Italiya, zai zama na bakwai da West Ham ta saya a bana.
Kungiyar da David Moyes ke jan ragama tana ta karshe a teburin Premier ba tare da maki ba, bayan wasa uku da ta buga.
Cikin 'yan wasan da ta dauka a bana da tsada har da mai cin kwallaye, Gianluca Scamacca daga Sassuolo kan fam miliyan 30 da mai tsaron baya Nayef Aguerd daga Rennes kan fam miliyan 30 da mai cin kwallaye Maxwel Cornet daga Burnley kan fam miliyan 17.5.
Haka kuma ta dauki mai taka leda daga tsakiya Flynn Downes daga Swansea kan fan miliyan 12 da mai tsaron baya Thilo Kehrer da mai tsaron raga Alphonse Areola da kudinsu ya kai fam miliyan 10 daga Paris St-Germain.











