Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan wasan Man United da Newcastle
Manchester United da Newcastle United za su kara a wasan karshe a Carabao Cup ranar Lahadi a Wembley.
Newcastle da United sun tashi 0-0 ranar 16 ga watan Oktoban 2022 a wasan farko a Premier League a Old Trafford a bana.
United ta kawo wannan matakin, bayan da ta doke Nottingham Forest 5-0 gida da waje a wasan daf da karshe, ita kuwa Newcastle cin Southampton 3-1 ta yi.
Wannan shi ne karon farko da kowacce kungiya ke fatan daga kofi a bana, karon farko da Newcastle ta kai karawar karshe bayan 1999.
Rabon da United ta dauki kofi tun kakar 2016/17 lokacin da ta lashe League Cup da Europa League karkashin Jose Mourinho.
Sai dai kungiyar Old Trafford ita ce kadai a Ingila da ke takarar lashe kofi hudu a kakar nan, bayan Carabao Cup da ta kai wasan karshe tana buga FA Cup.
Haka kuma tana ta uku a teburin Premier League, sannan ta kai zagayen 'yan 16 a Europa League, wadda za ta fafata da Real Betis gida da waje nan gaba.
Ranar Alhamis United ta yi waje da Barcelona da ci 2-1 a Old Trafford a karawar cike gurbin 'yan 16 a Europa League, wadda ta kai zagayen gaba 4-3 gida da waje.
Newcastle United ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Manchester United a 1999 a FA Cup a Wembley.
Kofi na karshe da Newcastle ta dauka shine a 1969, wadda ta lashe Inter-Cities Fairs Cup, kusan shekara 54 da ta wuce kenan.
Newcastle tana ta biyar a teburin Premier da tazarar maki daya tsakaninta da Tottenham ta hudu, wadda za ta karbi bakuncin Chelsea ranar Lahadi a Premier.
Sai dai kungiyar ta Eddie Howe za ta yi wasan karshen ba tare da mai tsaron raga ba, Nick Pope, wanda aka yi wa jan kati a karawa da Liverpool.
To sai dai Bruno Guimaraes ya kammala hutun dakatar da shi da aka yi.
Newcastle za ta yi amfani da Loris Karius a raga, bayan da ta bayar da aron Karl Darlow.