Jana'izar Ebrahim Raisi cikin hotuna

An wallafa

Dukkanin hotunan suna ɗauke da haƙƙin mallaka.

Gawar Ebrahim Raisi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana gudanar da jana'izar Ebrahim Raisi, tsohon shugaban Iran, wanda ya rasu ranar Lahadi a hatsarin jirgin sama lokacin da yake balaguro tare da wasu mutum bakwai.
Jana'izar Raisi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana gudanar da jana'izar ne a birnin Tabriz da ke Gabashin Azerbaijan.
Jana'iza

Asalin hoton, REX/Shutterstock

Bayanan hoto, A ranar Lahadi ne da yamma jirgin helikwaftan da suke ciki ya yi hatsari a yankin Gabashin Azerbaijan da ke kusa da iyakar Iran da Azerbaijan.
Jana'iza

Asalin hoton, REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Dubban Iraniyawa ne suka fito don yin bankwana da gawar shugaban, wanda sai a ranar Litinin aka sanar da rasuwarsu bayan gano ɓaraguzan jirgin.
Jana'iza

Asalin hoton, REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Wasu daga cikinsu sun yi nasarar kaiwa ga gawar marigayan.
Jana'iza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayan shugaban ƙasar, akwai kuma manyan jami'an gwamnati kamar Ministan Harkokin Waje Hossein Amirabdollahian, da Babban Limamin Tabriz Muhammad Ali Al Hashem.
Jana'iza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sauran sun haɗa da Gwamnan Gabashin Azerbaijan Malik Rahmati, da Kwamandan Dakarun Fadar Shugaban Ƙasa Mehdi Mousavi.
Jan'iza

Asalin hoton, REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Cikin masu makokin akwai mata sanye baƙaƙen kaya, tuni aka ayyana makokin kwana biyar a Iran ɗin.
Jana'iza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kazalika, an ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutun a ƙasar saboda a ranar ne za a yi jana'izar Raisi a hukumance a birnin Tehran.