Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasannin Afirka: Dama ta musamman ga mai masaukin baƙi Ghana
- Marubuci, Isaiah Akinremi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- An wallafa
Yayin da Ghana ke shirin karɓar baƙuncin gasar wasannin Afirka da aka jinkirta a shekarar 2023, masu shirya wasannin cikin gida sun kwara ruwan sanyi kan fargabar da ake yi, inda suka ce ƙasar ta shirya tsaf domin gudanar da gasar wasannin.
An ɗage wasannin da aka shirya gudanarwa a watan Agustan shekarar 2023 saboda rashin daidaito da aka samu kan haƙƙin tallace-tallace wanda ya kawo tsaikon kammala filayen gudanar da wasannin, tare da rashin jituwa tsakanin ƙungiyoyin da suka haɗa da masu shirya gasar, da ta tarayyar Afrika (AU), da Ƙungiyar kwamitocin Olympics na Afirka (Anoca) da kuma Ƙungiyar hukumomin Wasannin Afrika.
Duka ƙungiyoyi uku na taka muhimmiyar rawa wajen shirya gasar wanda a yanzu aka shirya za a fara ta da bikin buɗe gasar a Accra a ranar 8 ga Maris, a kuma kammala ranar 23 ga watan na Maris.
Dan Kwaku Yeboah, mai magana da yawun kwamitin shirya wasannin na Afirka (LOC), ya shaida wa BBC cewa "Wannan wata dama ce ta musamman a gare mu, mu ƙasar Ghana."
“An fara gudanar da wasannin Afirka ne tun a shekarar 1965, kuma in ban da Najeriya babu wata ƙasa ta yammacin Afirka da ta samu damar karɓar baƙuncin gasar.
Yeboah ya ƙara da cewa "Muna shirye daga kowane ɓangare: daga ababen more rayuwa da masauki da sufuri da kafofin watsa labarai. Kowane tsari yana kan hanya sai dai an ɗan jinkirta aikin tantancewa."
Ɗaya daga cikin tawagogin da tafiyar hawainiyar tantancewar ta shafa ita ce ƙasar Kamaru, wanda ƴan wasa da jami'anta da na kafofin yaɗa labarai suka fuskanci ƙarancin lokaci wurin tabbatar da matsayinsu a Ghana.
"Da farko jami'in mu ya samu ƴan matsaloli wajen fahimtar yadda ake aiki da dandalin tantancewar, amma yayin wani zama da ya yi da LOC ta Intanet, an ba shi haske kan yadda dandalin ke aiki," kamar yadda sakataren kwamitin wasannin Olympic na Kamaru David Ojong ya shaida wa BBC Sport Africa.
Yayin da ake shirin fara gasar a hukumance ranar Juma'a, an kuma nuna damuwa kan yadda Ghana za ta iya gudanar da wasannin.
Duane Dell'Oca mai sharhi kan harkokin wasanni na Afirka ta Kudu ya shaida wa BBC cewa, "Har wani ɓangaren filin motsa jiki ya fara lalacewa inda ya fara nuna alamun tsagewa, kuma makonni kaɗan da suka gabata aka shimfiɗa shi."
Ya kara da cewa "da alama waɗanda suke atisayen bikin bude gasar ne suka lalata shi."
Rashin halartar manyan taurarin Afirka
An tabbatar da wasanni 29 a gasar wasannin ta Afrika, da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan ƙwallon badminton, da tseren keke, da ninƙaya, da wasan tennis, da kuma kokawa, domin zama na masu neman cancantar shiga gasar Olympics a birnin Paris 2024.
Duk da haka, lokacin gudanar da wasannin na nufin da yawa daga cikin fitattun masu fafatawa a Afirka ba za su halarta ba - wannan babbar matsala ce ga waɗanda ke tallata gasar, a cewar Dell'Oca.
Dell'Oca ya ce "Ba su samu damar tallata hotunan manyan ƴan wasan Afirka da yawa ba saboda an samu ruɗani sosai kan waɗanda za su fafata a gasar."
Tsohuwar ƴar wasan Volley Ball ta Kenya Jannet Wanja, wadda a yanzu ita ce mai horar da ƴan wasan ƙasar, ita ma ta koka kan rashin samun halarcin manyan taurarin ƴan wasa.
"A lokuta da yawa wasannin sun samu koma baya saboda rashin manyan ƴan wasa da taurari da za su iya karawa gasar daraja. Sau da yawa ana hana manyan ƴan wasa zuwa. Hakan ba ya taimakawa. Mu ma muna da mahimmanci a matsayinmu na ƴan Afirka," kamar yadda ta shaida wa BBC Sport Africa.
Sai dai duk da ƙalubalen da ake fuskanta a gasar, tana da ƙwarin gwiwar samun nasarar gudanar da gasar wasannin Afirka a Ghana.
Wanja ta ƙara da cewa "Yawancin ƙasashe har yanzu suna fama da tasirin cutar korona kuma matakan shirye-shiryensu sun yi ƙasa da abin da ake buƙata, amma har yanzu ina fatan samun nasarar gasar."
Ojong ya ce, duk fargabar da ake yi game da filayen wasa da kayan aiki, dukkanin ƙungiyoyi za su fuskanci batutuwa iri ɗaya.
"Idan LOC da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun tabbatar da cewa filayen sun dace da wasa, dole ne tawagogi su yi wasa a filayen yadda su ke." in ji shi.
"Kowa zai yi wasa a wuri guda, kowa zai fukanci matsaloli iri ɗaya, kuma hakan zai zama wani ɓangare na wasan."
Ana matuƙar farin ciki a Accra
Bayan murnar gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala kwanan nan a ƙasar Ivory Coast, Yeboah ya ce ya kamata ƴan kallo da ƴan wasa da jami'ai su sa rai cewa za a gudanar da gasar da ba za a manta da ita ba a nahiyar Afirka.
"Ya kamata Afirka ta yi tsammaci irin karamci da al'adun Ghana da aka saba gani - su yi tsammanin za a gudanar da bikin buɗe gasa mai matuƙar ƙayatarwa
"Ya kamata su kyautata zaton ganin wasanni masu ƙayatarwa da kuma kyakkyawar yanayi a tattare da gasar saboda ƴan Ghana na cikin matuƙar farin ciki."
Ana sa ran manyan wakilan ƙungiyar AU da shugabannin ƙasashe daban-daban da kuma ƴan wasa sama da 5,000 da jami'ai daga sassan nahiyar su halarci gasar wanda za a shafe tsawon mako biyu ana gudanarwa.