Ghana ta kori kocinta bayan fitar da ita daga Afcon

An wallafa

Ghana ta kori kocinta Chris Hughton bayan da aka fitar da kasar a matakin rukuni na gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta kasashen Afirka, Afcon 2023.

Kungiyar ta Black Stars ta kammala wasanta a rukunin B da maki biyu inda ta yi canjaras da Masar da Mozambique da biyu da biyu. Ta yi rashin nasara a wasanta na farko a hannun Cape Verde da 2-1.

Ghana tana da burin tsallakawa mataki na gaba sai dai an yi waje rod da ita a ranar Talata bayan an doke ta.

An nada Hughton a matsayin kocin Ghana cikin Fabarairun bara.

"An sallami Chris Hughton nan take," kamar yadda wata sanarwa daga hukumar kwallon kafa ta Ghana GFA ta sanar.

"Shugabancin hukumar ya kuma dauki matakin rushe tawagar masu horaswa na kungiyar ta Black Stars.

"GFA, a yan kwanaki masu zuwa za ta samar da taswira kan inda Black Stars za ta sa gaba."

Hughton wanda tsohon kocin Newscastle da Brighton ne ya soma aiki a matsayin kocin kungiyar a Fabarairun 2022.

Ghana ta taɓa lashe kofin Afcon sau hudu a tarihi.

Ya maye gurbin Otto Addo da ya yi murabus bayan gasar cin kofin duniya ta 2022 da Ghana ta zo ta karshe a rukunin H inda ta yi nasarar wasa ɗaya daga uku da ta buga.

A gasar Afcon ta 2021 da aka yi a Kamaru, Ghana ta fice a matakin rukuni.

Hukumar ta GFA ta ce tana "goyon bayan Hughton dari bisa dari bayan da sa-in-sa ta shiga tsakaninsa da wani mai goyon bayan kungiyar kan rashin nasarar da Black Stars ta yi a hannun Cape Verde.

Da farko ana tunanin kocin mai shekara 65 zai taimaka wa Black Stars wajen tsallakawa mataki na gaba inda Ghana ta zo ta biyu a rukunin B - ta kere Mozambique da maki biyu a wasan karshe na matakin rukuni.

Sai dai Mozambique ta zura kwallo biyu ana gab da tashi wasa inda ta yi canjaras abin da kuma ya aika kungiyar Ghana gida.