Ronaldo ba ya jin dadin zaman bencin da yake in ji Ten Hag

An wallafa

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce Cristiano Ronaldo ba ya jin dadin rashin buga wasan da yake a kungiyar.

Ronaldo, mai shekara 37, sau daya ya buga wasan Premier ya kuma buga wasa biyu a Europa a wannan kakar.

Ba a yi amfani da shi ba a wasan da kungiyar ta buga a City wanda ta sha kashi da 6-3, yayin da Ten Hag ya ce yaki sa shi ne "saboda kada a wulakanta mutuncin dan wasan".

"Bai ji dadi ba na rashin buga wasan ranar Lahadi" ya ce in ji Ten Hag gabanin wasan da za su buga a Omonia Nicosia.

"Tabbas yana son ya rika buga wasa, kuma yana jin babu dadi idan bai buga wasa ba, abu ne a zahiri."

Ten Hag ya kara da cewa: "Amma ina fada maka cewa duka 'yan wasa da ke nan suna cikin farin ciki da jindadi, kuma lokacin da kake benci ba zaka ji dadi ba, to kaga nan ba kungiyar da zaka ci gaba da zama ba ce, musamman Cristiano.

"Mutum ne mai son gasa kamar yadda duk muka sani. Tabbas baya farin ciki idan baya buga wasa.

"Na fada na sake cewa, yana atisaye yadda ya kamata, kuma yana cikin yanayi mai kyau, yana karfafa gwiwar yan wasa da yawa. kuma dama haka muke tsammani daga gare shi.

Tsohon Kyaftin din kungiyar Roy Keane ya sha sukar Ten Hag kan ajiye Cristiano a benci, yana cewa wannan "rashin girmamawa" ne ga dan wasan.

Ten Hag ya amince cewa akwai bukatar a tafiyar da Ronaldo ta hanya ta musamman.

"Idan zamu fadi gaskiya, mun san cewa kowa na da nasa banbancin.

"Ko wa na da na shi banbancin, kuma zan yi aiki da kowa cikin girmamawa tunda suna da banbanci a tasowarsu.

"Amma akwai doka da zata yi aiki akan kowa".