Barcelona gidan Messi ne a koda yaushe - Laporta

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba, Joan Laporta ya ce Barcelona gidan Lionel Messi ne, bayan da kungiyar ke kokarin sake daukar dan wasan a karshen kakar nan.
Kwantiragin kyaftin din Argentina zai kare a Paris St Germain a karshen watan Yuni, inda wasu rahotanni ke cewar zai koma Saudi Arabia da taka leda.
Sai dai a wata hira da kafar yada labarai ta Sifaniya TV3, Laporta ya ce za su kalubalanci duk kungiyar da ke son sayen dan wasan mai shekara 35.
''Tarihi zai goyi bayanmu, muna da fata mai karfafa gwiwa, muna da magoya baya miliyan 400 a duniya'' in ji Laporta.
Messi ya bar Camp Nou shekara biyu da ta wuce, bayan kaka 21 a kungiyar, amma ya ci karo da cikas a kakar farko a Faransa.
A karshen mako magoya bayan PSG suka yi masa ihu a karawa da Ajaccio, bayan da ya koma buga tamaula, sakamakon dakatar da shi saboda zuwa Saudi Arabia ba tare da izini ba.
Laporta ya ce akwai alaka mai girma tsakaninmu, inda ya ce ya taya Messi murnar lashe kofin duniya, wanda Argentina ta lashe a bara a Qatar.
''Yanzu dan kwallon PSG ne, saboda haka za mu jira zuwa karshen kakar nan, idan yarjejeniyarsa ta kare, daga nan mu shiga batun cinikinsa.
''Tare da kalmar girmamawa ga Saudi Arabia, Barca dai Barca ce, kuma gidan Messi ne.''
Wadan nan kalaman sun zo ne, bayan da Barcelona ta lashe La Liga na farko a kaka hudu, bayan da ta ci Espanyol 4-2 ranar Lahadi.










