Man United ta ci Forest da kyar da gumin goshi a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta doke Nottingham Forest da ci 3-2 a wasan mako na uku a gasar Premier ranar Asabar a Old Trafford.
Minti biyu da fara wasa Taiwo Awoniyi ya ci wa Forest kwallo, sannan minti biyu tsakani Willy Boly ya ci na biyu.
Kenan Awoniyi ya ci kwallo a wasa na bakwai a jere a Premier League a Nottinhgam Forest, ya fice tarihin da Stan Collymore ya yi wa kungiyar a 1995.
Kuma shi ne dan wasan Forest na farko da ya ci kwallo a kowanne wasa uku da fara kakar bana tun bayan bajintar Peter Davenport a 1984-85.
Haka kuma Awoniyi ya zama bakar fata na uku da ya ci kwallo a wasa bakwai a jere a Premier League, bayan Emmanuel Adebayor da kuma Mohamed Salah.
Tun kan hutu United ta zare daya ta hannun Christian Eriksen a minti na 17, sannan Casemiro ya farke na biyu a zagaye na biyu a karawar.
United ta ci na uku da ya ba ta maki ukun da take bukata ta hannun Bruno Fernandes, bayan da aka yi wa Marcus Rashford keta a da'ira ta 18. Sai dai tun kafin nan an bai wa Joe Worrall jan kati, inda Forest ta karasa fafatawar da 'yan wasa 10 a ciki fili.
United, wadda ta ci Wolves 1-0 a wasan farko da fara Premier League ta kakar nan ta yi rashin nasara a hannun Tottenham da ci 2-0 a karawar mako na biyu.












