Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Watakila Aubameyang ya fara buga wa Chelsea wasa a Zagreb
Watakila Pierre-Emerick Aubameyang ya fara buga wa Chelsea tamaula a wasan farko a rukuni na biyar da za ta ziyarci Dinamo Zagreb a Champions League ranar Talata.
Kociya Thomas Tuchel ya fada cewar ''ya dauko dan kwallon domin ya nuna kansa'' bayan da ya koma Stamford Bridge kan £10.3m a ranar karshe da aka rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bana ranar Alhamis.
Aubameyang zai saka fuskar roba domin kariya, bayan raunin da ya ji a lokacin da 'yan fashi suka shiga gidan da yake a makon jiya a Sifaniya.
Mintuna takwas kadai dan kwallon Gabon ya yi wa Barcelona a kakar nan.
Tuchel ya tabbatar da cewar Chelsea ta ziyarci Zagreb tare da sabon dan wasan da ta dauka Denis Zakaria.
Sai dai dan wasan Brazil, mai shekara 37, Thiago Silva na Ingila don ci gaba da murmurewa.