Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ilele Garkuwan mai Caji ya doke Shagon Makwa
An wallafa
Ilele Garkuwan mai Caji ya buge Shagon Makwa a damben Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke DeiDei a Abuja, Najeriya.
Ilele dan damben Kudu ya yi nasara a kan dan wasan Arewa a turmi na biyu, inda Shagon Makwa ya fadi kasa wanwar har sai da Ilele ya tsallaka shi.
Sauran wasannin da aka yi kisa:
- Zazu daga Kudu ya buge Dogon Awilu Guramada
- Shagon dan Gero Guramada ya doke Shagon dan Malumfashi daga Arewa
- Kwaro daga Arewa ya yi nasara a kan Dogon Maiduguri
- Dogon Autan Mamman ya buge Dogon Maiduguri
- Shagon Lawwali daga Jamus ya doke Shagon Matawalle
Wasannin da aka yi canjaras
- Bagobiri Guramada da Shagon Musan Kaduna
- Autan Ali Kanin Bello da Biyun Sama'ila
- Dan dabar Autan dan Bunza daga Arewa da Shagon dan Gero Guramada