Ronaldo ya ci kwallo ta farko a Europa 

An wallafa

Ronaldo ya kawo karshen kamfar kwallayen da yake yi, yayin da ya ci kwallonsa ta farko a Europa a tarihi biyo bayan nasarar da Manchester United ta samu a Sheriff Tiraspol.

Kungiyar ta yi rashin nasara har gida a wasanta na farko a Old Trafford wanda ta buga da Real Sociedad, sai dai kuma ta dawo da karfinta inda ta samu nasara a Moldova.

Red Devils sun fara cin kwallon farko ne cikin yanayi na nutsuwa gabanin tafiya hutun rabin lokaci bayan da Christian Eriksen ya bai wa Jadon Sancho kwallo ya ci.

Tun da safiyar ranar Alhamis aka sanar da cire Sancho daga cikin tawagar Ingila.

Sun kara kwallo ta biyu ne tav hannun Cristiano Ronaldo bayan bugun daga kai sai mai tsaron raga da United ta samu.

Patrick Kpozo ne ya doke Diogo Dalot a cikin yadi na 18.

A karshe dai United ta kare wasan ba tare da an jefa mata kwallo ko daya a raga ba.