Man United ta tsawaita kwantiragin Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images
Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, Ruben Amorim, ya tabbatar da tsawaita kwantiragin Harry Maguire.
Yayin da yake jawabi a taron manema labarai, Mista Amorim ya ce ƙungiyar ta tsawaita kwantiragin ɗanwasan da shekara ɗaya.
Ɗanwasan bayan mai shekara 31, ya koma United daga Leicester City a shekarar 2019, kuma a wannan kakar kwantiraginsa zai ƙare, amma yanzu zai ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa watan Yunin 2026.
Maguire ya yi wa United wasa 222 tare da cin ƙwallo 12, sannan ya taimaka wa ƙungiyar lashe manyan kofuna biyu na Carabao a 2023 da FA a 2024.
Ɗanwasan na Ingila ya yi wasa bakwai ƙarƙashin sabon koci Amorim, kuma yadda ya iya salon buga wasa da 'yanwasan baya uku a Ingila ya ba shi damar haskawa a tsarin sabon kocin, musammnan a nasarar da United ta samu kan Man City a wasansu na baya-bayan nan.
Haka nan, Amorim ya tabbatar da cewa akwai wasu 'yanwasan da ke dab da tsawaita kwantiraginsu.








