Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Camavinga ya buga wa Real Madrid wasan La Liga na 100
Ranar Asabar Real Madrid ta je ta shi 3-3 a gidan Rayo Vallacano a gasar La Liga mako na 17 da suka kara a Vallecas Stadium.
Camavinga ya buga wasan, kuma na 100 kenan da ya yi wa Real Madrid a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Sai dai ɗan wasan tawagar Faransa ya yi karawa ta 155 a ƙungiyar ta Santiago Bernabeu a dukkan fafatawa, wanda aka ci wasa 71 da shi.
Mai taka leda daga tsakiya ya lashe kofin La Liga biyu a 2022 da kuma a 2024 a Real, tun bayan da ya koma Santiago Bernabeu kaka huɗu da ta wuce.
Cikin wasa na 100 da ya yi a La Liga, kungiyar da yafi fuskanta ita ce Osasun, wadda suka ɓarje gumi karo bakwai da Camavinga.
Haka kuma a dai wasannin La Liga, kakar da ya buga fafatawa da yawa ita ce ta 2022/23, wanda ya buga wasa 37.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 38 iri ɗaya da na Barcelona ta ɗaya, wadda za ta karɓi bakuncin Leganes ranar Lahadi.
Ranar Lahadi 22 ga watan Disamba Real Madrid za ta kara da Sevilla, sannan ta je gidan Valenci ranar Juma'a 3 ga watan Janairun 2025 a dai La Liga.