Eskas ne zai busa wasan Barcelona da Dortmund a Champions League

Espen Eskås

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

UEFA ta sanar da naɗa ɗan kasar Norway, Espen Eskas a matakin shi ne zai yi alkalancin wasan Barcelona da Borussia Dortmund ranar Laraba.

Barcelona ce za ta kara da Dortmund a Sifaniya a wasan farko zagayen kwata fainal a Champions League.

Eskas fitatce ne a fagen alkalancin tamaula a Turai, wanda ya samu lasisi tun daga 2017, kuma Dennis Higler daga Netherlands zai kula da VAR a wasan na Laraba.

Wannan shi ne karo na bakwai da Eskas zai yi rafli a Champions League a kakar nan, har da huɗu da ya busa a fafatawar cikin rukuni.

Haka kuma karo na biyu da zai yi rafli a wasan Barcelona a bana, wanda shi ne ya busa wasan da ta doke Red Star Belgrade 5-2.

Sai dai Barcelona ba za su manta da Eskas ba, wanda ya yi rafli a karawar da tawagar Sifaniya ta ƴan shekara 21 ta yi rashin nasara a hannun ta Ingila 1-0 a gasar kofin nahiyar Turai ba.

Haka kuma shi ne ya busa wasan da tawagar Brazil ta mata ta doke ta Sifaniya 4-2 a Paris Olympic a 2024.