Ana kai wa Isra'ilawan da suka je kallon Europa hari a Netherland

B

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ajax ta doke Maccabi Tel Aviv 5-0 a wasan na gasar Europa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomin Isra'ila da na Netherland sun yi tir da hare-haren da aka kai wa magoya bayan kallon ƙafar Isra'ila a daren jiya a Masterdam.

Magoya bayan Maccabi Tel Aviv sun riƙa fuskantar hari a birnin lokacin da kungiyarsu ta je buga wasan Europa da Ajax.

'Yan sanda a Amsterdam sun kama mutum aƙalla 62.

Hotona da bidiyo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda aka riƙa kai wa Isra'ilawa hare-hare a kan titina, da yadda mutane suke kutsa kai cikin otel suna neman magoya bayan Maccabi.

A

Asalin hoton, EPA

Dama tun gabanin wasan an samu rikici da masu goyan bayan Falasɗinawa da magoya bayan Maccabi, mutane da dama suka riƙa cinna wuta suna sa hayaki mai sa hawaye da kuma ɗaga tutar Falasɗinawa a wani titi da ke kusa.

Firaiministan Netherland Dick Schoof ya yi tir da "harin nuna kin jinin Yahudawa", yayin da shi kuma na Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za a aike da "jiragen ceto" domin kwaso magoya bayan da abin ya rutsa da su a Amsterdam.

A

Asalin hoton, EPA

Babu abin da ya shafe mu da yaƙin da ake yi

h

Asalin hoton, Reuters

Magoya bayan Isra'ila biyu wadanda suka je Amsterdam kallon wasa sun ce rikicin abin tsoro ne.

Da suke bayani a bakin dandalin taro na Dam Joni Pogrebetsy ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun ga yadda aka riƙa kai hare-hare a bakin dandalin lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa otel.

Ya ce mai gidan abincin da suka je sai da ya ja musu kunne kan rikicin, wanda ya ce zai ba su wurin buya kan rikcin ya lafa.

Pogrebetsy ya ce 'yan sanda sun je wurin a ƙurarren lokaci, bayan an raunata mutane masu yawan gaske.

Jami'ai a Netherland sun ce an girke 'yan sanda masu yawa a birnin tun gabanin wasan da kuma bayan an tashi.

Michael Asuss, wanda yake zaune a Netherlands wanda ya je kallon wasan, ya ce wadanda ake kai wa hari ba su da ruwa da yaƙin da Isra'ila dake yi a Gabas ta Tsakiya a yanzu.