Man United za ta kara da Leicester a FA Cup zagaye na huɗu

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta karɓi bakuncin Leicester City a FA Cup zagaye na huɗu a cikin watan Fabrairu.
United mai rike da kofin ta kai wannan matakin bayan da ta doke Arsenal 5-3 a bugun fenariti ranar Lahadi a Emirates.
Tun farko sun tashi 1-1 har da karin lokaci a wasan da United ta kare da ƴan wasa 10, sakamakon da aka bai wa Diago Dalot jan kati a karawar ta hamayya.
A jadawalin da aka fitar ranar Lahadi, Liverpool, wadda take ta ɗaya a kan teburin Premier League za ta kece raini da Plymouth Argyle.
Argyle, wadda take karshen teburin Championship a bana ta yi nasarar yin waje da Brentford mai buga Premier League da cin 1-0 ranar Asabar.
Wadda take ta ɗaya a kan teburin League 1, Birmingham za ta karɓi bakuncin Newcastle United, yayin da za a fafata tsakanin Exeter da Nottingham Forest.
Akwai wasa da za a buga a FA Cup tsakanin ƙungiyoyin da ke buga Premier, shi ne Tottenham da Aston Villa, Brighton da Chelsea da na Bournemouth da Everton.
Manchester City za ta je gidan Leyton Orient ko kuma Derby County, yayin da Crystal Palace da Doncaster za su fafata a tsakaninsu.
Za a buga wasannin ranar Asabar 8 ga watan Fabrairu
Jadawalin zagaye na huɗu a FA Cup na bana:
- Manchester United da Leicester City
- Leeds United da Millwall ko kuma da Dagenham and Redbridge
- Brighton & Hove Albion da Chelsea
- Preston North End ko Charlton Athletic da Wycombe Wanderers
- Exeter City da Nottingham Forest
- Coventry City da Ipswich Town
- Blackburn Rovers da Wolverhampton Wanderers
- Mansfield Town ko Wigan Athletic da Fulham
- Birmingham City da Newcastle United
- Plymouth Argyle da Liverpool
- Everton da Bournemouth
- Aston Villa da Tottenham Hotspur
- Southampton da Burnley
- Leyton Orient ko Derby County da Manchester City
- Doncaster Rovers da Crystal Palace
- Stoke City da Cardiff City











