Real ta koma ta biyu a teburin La Liga

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta doke Rayo Vallecano 2-1 a wasan mako na 27 a La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Kylian Mbappe ne ya fara cin ƙwallo a minti na 30, sai Vinicius Junior ya kara na biyu a minti huɗu tsakiya.

Sai dai daf da hutu Rayo Vallecano ta farke ta hannun Pedro Diaz.

Kawo yanzu Mbappe yana da hannu a cin ƙwallaye a wasa shida a gida a La Liga, wanda ya ci shida ya bayar da biyu aka zura a raga.

Haka kuma Real Madrid ta zura ƙwallo a raga a wasa 25 daga 27 da ta buga a kakar nan, ita kaɗai ce da wannan ƙwazon.

Ita kuwa Rayo Vallecano ta kasa cin wasa daga karawa huɗu baya a La Liga ta taɓa yin wasa tara ba tare da yin nasara ba daga 20 ga Janairu 2024 zuwa 10 ga watan Maris 2024.

Da wannan sakamakon Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga mai ƙwantan wasa da maki 57, iri ɗaya da na Real Madrid ta biyu, sai Atletico ta uku mai 56.

Atletico Madrid ta ɓarar da damar hawa kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, bayan da Getafe ta doke ta 2-1 ranar Lahadi.

Ranar Laraba 12 ga watan Mayu, Real Madrid za ta je Atletico Madrid a wasa na biyu a Champions League, wasan farko RReal ce ta ci 2-1.

Daga nan Villareal ta ta karɓi bakuncin Real Madrid a La Liga ranar Asabar 15 ga watan Maris.